Kotun koli za ta ta yanke hukuncin Kujerar Gwamnan Kogi a Jumu'a

Kotun koli za ta ta yanke hukuncin Kujerar Gwamnan Kogi a Jumu'a
 
Kotun ƙolin Nijeriya ta shirya gabatar da hukuncin Shari'ar da ke gabanta a gobe Jumu'a karar da Murtala Yakubu Ajaka na jam'iyyar SDP ya sanya a gabanta kan zaɓen 2023 wanda ya baiwa APC nasara.
Hukuncin zai tabo maganar BVAS a zaɓen Nuwamba 11, 2023 da aka yi a Kogi.
 

A jawabin da SDP ta fitar ta gayyaci magoya bayan jam'iyyar da su halarci zaman kotun don an yi hukunci a gabansu.

Bayanin wanda Isaiah Davies Ijele, daraktan yada labarai na zamani a kwamitin kamfe ya nuna kwarin guiwarsa da mutane su halarci  zaman domin lamari ne na dimukuradiyya.