Kotun Koli Ta Shirya Yanke Hukuncin Shari'ar Atiku Da Tinubu

Kotun Koli Ta Shirya Yanke Hukuncin Shari'ar Atiku Da Tinubu

 
Kotun koli ta sanar da cewa ta shirya yanke takaddama na shari'ar zaben shugaban kasa a mako mai zuwa. Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP na kalubalantar zaben Shugaba Tinubu da aka gudanar a watan Faburairu na wannan shekara, Legit ta tattaro. 
A yau Alhamis 19 ga watan Oktoba kotun kolin ta tura sanarwar ga lauyoyin masu kara da ma su kare kansu a shari'ar.
Kotun koli ta sanar da ranar Litinin 23 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta yanke hukuncin zaben shugaban kasa a Abuja, The Nation ta tattaro. A farkon watan Satumba ne kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa ta yi watsi da korafin 'yan jam'iyyun adawa. Kotun ta watsar da korafin 'yan takarar jam'iyyun PDP, Atiku Abubakar da Labour, Peter Obi 
Bayan yanke hukuncin, Atiku ya daukaka kara zuwa kotun koli don kwato hakkinsa da aka tauye ma sa. A dalilin haka, Atiku ya binciko badakalar takardun Tinubu na Jami'ar Chicago da ke Amurka. Tun farko, tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci kotu ta tilasta Jami'ar mika ma sa takardun karatun Tinubu da ake cece-kuce a kansu. Ana shi bangaren, Obi shi ma ya daukaka kara a kotun koli inda ya bukaci kotun ta yi fatali da hukuncin kotun a baya.