Home Finafinnai Kotun Kano ta ɗaure jarumar Kannywood Samha Inuwa wata 6

Kotun Kano ta ɗaure jarumar Kannywood Samha Inuwa wata 6

14
0

Kotun Kano ta ɗaure jarumar Kannywood Samha Inuwa wata 6, ko zabin tarar N200,000

Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke wa jarumar Kannywood, Samha Inuwa, hukuncin daurin watanni shida bayan samunta da laifin cin zarafin takardun kudin naira, lamarin da ya fito fili a wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta.

Hukumar EFCC ce ta kama ta tare da gurfanar da ita bisa karya dokar Babban Bankin Najeriya da ta haramta lalata ko wulakanta kudin kasa, inda kotu ta kuma ba ta zabin biyan tarar N200,000 maimakon zaman gidan yari.

Hukuncin ya sake jaddada gargadin hukumomi cewa duk wanda aka samu da cin zarafin naira zai fuskanci tsauraran matakan doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here