Kotun Daukaka Kara Za Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Tambuwal Da Kuma Ta Wamakko
Kotuun daukaka kara dake Abuja, a gobe Talata 19 ga watan Disamba zata yanke hukunci kan shara'ar dake tsakanin Sanata Aminu Waziri Tambuwal da kuma tsohon sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba Dambuwa kan zaben 2023 da aka gudanar.
Haka ma duk a gobe Talata, kotun zata yanke hukunci kan shara'ar dake tsakanin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da kuma tsohon mataimakin Gwanna na jahar Sokoto Manir Muhammad Dan'iya.
Hukuncin na gobe zai kawo karshe Shari'ar da ke tsakanin mutanen biyu kan abin da ya shafi zaben da ya gabata.
managarciya