Kotun ɗaukaka kara ta umarci ASUU ta janye yajin aiki kuma malamai su gaggauta koma wa aiki

Kotun ɗaukaka kara ta umarci ASUU ta janye yajin aiki kuma malamai su gaggauta koma wa aiki

 

Kotun ɗaukaka kara ta umarci Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU da ta janye yajin aikin, inda ta ce haka ne kawai sharadi da bukatar kungiyar ta daukaka kara kan hukuncin kotun masana’antu ta kasa da ta umarci kungiyar ta janye yajin aikin za tayi tasiri.

 
Sai dai kuma kotun ta amince da bukatar ne bisa sharadin cewa kungiyar ta yi biyayya ga hukuncin da kotun kasa ta yanke,  sannan kuma ta janye yajin aikin nan take har zuwa lokacin da za a yanke hukunci.
 
Kotun ta baiwa ASUU wa’adin kwanaki bakwai da ta shigar da kara, biyo bayan biyayya ga hukuncin da karamar kotu ta yanke.