Kotu  Za Ta Iya Hana Bola Tinubu da Sauran ‘Yan  APC Tsayawa Takara a 2023

Kotu  Za Ta Iya Hana Bola Tinubu da Sauran ‘Yan  APC Tsayawa Takara a 2023

APC ta damu da hukuncin da babban kotun tarayya mai zama a Abuja tayi na ruguza tsaida Isiaka Oyetola a matsayin ‘dan takarar Gwamnan Osun. Rahoton Tribune yace ‘Ya ‘yan jam’iyyar APC su na jin tsoron wannan hukunci da Alkali ya yi a kan Isiaka Oyetola da mataimakinsa su shafi zaben 2023.

Kotu tace shiga takararsu Isiaka Oyetola a zaben Gwamnan Osun ya ci karo da doka da tsarin mulki domin Mai Mala Buni ne ya mikawa INEC sunayensu. 
Hukuncin da Alkali ya zartar shi ne dokar zabe da sashe na dokar kasa na 183 sun ce Buni bai isa ya rike kujerar shugaban jam’iyya alhali yana gwamna ba. 
Gwamnan jihar Osun ya yi alkawarin zai daukaka kara domin ayi watsi da wannan hukunci. Jaridar Sunday Tribune tace cikin ‘yan takara ya duri ruwa. 
Idan hukuncin Mai shari’a Emeka Nwite ya zauna, duk wani ‘dan takaran jam’iyyar APC da Mala Buni ya gabatarwa INEC sunansa, yana fuskantar barazana. 
Daga cikin ayyukan da gwamnan na Yobe yayi yana rike da kujerar shugabancin APC na rikon kwarya akwai ba Abiodun Oyebanji tikiti a zaben jihar Ekiti. Bugu da kari shi ya gudanar da zaben shugabannin jam’iyya na kasa har aka nada majalisar NWC. Za a samu makamancin wannan rahoto a shafin Nairaland.