Kotu za mu tafi, PDP ta yi watsi da sakamakon zaben Edo
Jam'iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon zaben gwamna na jihar Edo da dan takarar APC, Monday Okpebholo ya lashe.
Shugaban PDP na riƙo na ƙasa, Umar Damagum ne ya baiyana hakan a taron manema labarai a Abuja da ya gudana a yanzun nan.
Damagum ya jaddada cewa jam'iyyar za ta kwato hakkin ta a kotu tunda a cewar sa, mutanen Edo Dr Asue Igahlo na PDP su ka zaba.
Sakamakon zaɓen ya baiwa mutanen Nijeriya mamaki la'akari da mutane sun yi mamakin yadda sakamakon ya fita sabanin wanda aka zaba a zargin su.