Kotu tayi watsi da karar APC, ta tabbatar da nasarar Dauda Lawal A Zamfara

Kotu tayi watsi da karar APC, ta tabbatar da nasarar Dauda Lawal A Zamfara

Kotun sauraren kararrakin zaben gwamna dake zaman ta a jahar sakkwato a ranar litinin ta tabbatar da nasarar zaben Gwamna Dauda Lawal a matsayin gwamnan jahar Zamfara.
 
Wani ayarin lauyoyin dake karkashin jagorancin mai shari’a Cordelia Ogadi itace ta yanke hukuncin a yau din nan bayan karar da jam’iyar APC da dan takarar ta suka shigar a gaban ta.

Yayin da kotun take yanke hukunci akan nasarar Dauda Lawal na jam’iyyar PDP tace zaben da akayi masa yana cikin tanadin dokar hukumar zabe ta kasa INEC.

Idan dai ana iya tunawa jam’iyyar APC da Muhammad Matawalle wanda a yanzu shike zaman karamin ministan tsaron kasa sun zargi hukumar zabe ta kasa INEC bisa kin sanya wasu sakamakon zaben mazabu wanda yayi amannar cewa muddin aka sanya sakamakon nasu yana iya lashe zaben da gagarumin rinjaye.


To saidai da kotun ke yanke hukuncin hakama ta bukaci jam’iyyar APCn data biya tarar naira dubu dari biyar a matsayin bata lokacin kotu.