Kotu taki bada belin wanda ake zargi da wallafa sakamakon jarrabawar Gwamnan Sokoto

Kotu taki bada belin wanda ake zargi da wallafa sakamakon jarrabawar Gwamnan Sokoto

Wata kotun Majistiri dake Sokoto ta tura Shafi'u Umar Tureta zuwa gidan gyaran hali bisa zargin yiwa gwamnan jihar, Ahmad Aliyu da matarsa, Hajiya Fatima Ahmad Aliyi karya da cin zarafi a shafin sada zumunta.

 Tureta, wanda mataimaki ne na musamman ga Sanata Aminu Waziru Tambuwal, an tuhume shi da laifin yada kalaman batanci da karya.

A yadda takardar bayanan kara ta nuna, wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 18 ga watan Yuli na 2024.

Jami'in dan sanda dake gabatar da kara, Abdulrahman Mansur, ya shaidawa kotun cewa laifukan da wanda ake zargi ya aikata sun saba da kundin dokoki na shari'a.

Ana tuhumarsa ne da laifin yada bidiyon matar Gwamnan tana lika kudi a yayin taron bikin tunawa da ranar Haihuwa.

An kuma zargi Tureta da laifin yada wasu takardu dake nuna Gwamna Aliyu ya fadi darasin Turanci a jarrabawar kammala Sakandire da kuma yadda yake gaza yin magana da harshen na Turanci.

Sai dai yayin da aka karanta tuhumar, wanda ake karar ya musanta zarge-zargen, inda lauyansa, Barista Al'Mustapha ya nemi a bada belinsa.

Alkaliyar, kotun Fatima Hassan ta sanya yau Juma'a domin yanke hukunci kan bukatar bada belin.

Sai dai a zaman kotun na yau, Alkaliyar taki amincewa da bada belin.

Mai shari'ar ta dage zaman kotun zuwa 18 ga watan Satumba inda ta bada umarnin ci gaba da tsare wanda ake zargin.