Kotu ta yanke wa jarumar Kannywood Sadiya Haruna  hukuncin wata 6 a gidan yari ba zaɓi

Kotu ta yanke wa jarumar Kannywood Sadiya Haruna  hukuncin wata 6 a gidan yari ba zaɓi
Kotun Majistire, da ke zaman ta a Filin Jirgin sama na Kano, ta yanke wa wata jarumar Kannywood kuma shahararriyar mai amfani da kafar sadarwa ta instagram, Sadiya Haruna hukuncin ɗaurin watanni shida.
Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Muntari Dandago, ta yanke hukuncin ne ba tare da zaɓin tara ba.
An yanke wa Sadiya wannan hukuncin ne bisa kalaman ɓatanci da ta yi ga wani ɗan wasan kwaikwayo na Kannywood,  Isah I. Isah a shafinta na Instagram.
Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa tun a ranar 16 ga watan Oktoba, 2019 a ka fara grufanar da Sadiya a kotun.