Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta yi rajistar jam’iyyar National Democratic Party (NDP) a matsayin jam’iyyar siyasa kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
Mai shari’a Mohammed Umar, yayin yanke hukunci a ranar 16 ga Fabrairu, ya ce masu karar sun cika dukkan sharuddan da Kundin Tsarin Mulki da Dokar Zabe ta 2022 suka tanada domin rajista.
Kotun ta soke wasikar INEC ta ranar 18 ga Disamba, 2025, wadda ta ki amincewa da bukatar rajistar, tare da bayyana ta a matsayin mara inganci.
Alkalin ya umarci INEC ta yi rajistar jam’iyyar nan take, ta kuma ba ta dukkan hakkoki da takardun da ake bai wa jam’iyyun siyasa masu rijista.
Kotun ta kuma ce idan ba a aiwatar da rajistar ba, za a dauki NDP a matsayin wadda aka yi wa rajista bisa tanadin dokar zabe.





