Kotu ta tura Murja Kunya zuwa asibitin masu lalurar ƙwaƙwalwa
Join our subscribers list to get the latest news, updates and special offers directly in your inbox
Wata kotu da ke zaman ta a birnin Kano ta bayar da umarnin tura ƴar tiktok Murja Ibrahim Kunya zuwa asibitin masu taɓin hankali domin duba lafiyar ƙaƙwalwarta.
Mai magana da yawun kotunan jihar Kano, Babajibo Ibrahim ne ya tabbatar wa BBC hakan bayan zaman kotun da aka yi a yau Talata.
A hirar sa da BBC, Babjibo ya ce "yanayin da take ciki da kamannunta da kuma maganganun da take faɗa sun nuna cewa ba ta cikin hali na cikakken hankali."
Ya ƙara da cewa "wannan ne dalilin da ya sa alƙalin ya buƙaci a tura wadda ake zargin zuwa asibitin masu lalurar ƙwaƙwalwa har zuwa ranar 20 ga watan biyar, 2024."
Hukumar Hizba ta jihar Kano ce ta kama Murja Kunya tare da miƙa ta ga jami'an tsaro bisa zargin ta da laifukan da suka shafi baɗala a shafukan sada zumunta.
Kwamandan hukumar ta Hizba a jihar, Sheikh Ibrahim Daurawa ya ce tuhume-tuhumen da ake yi wa Murja Kunya sun haɗa da: Razana al'umma, ayyukan baɗala, tayar da hatsaniya, tayar da hankalin al'umma, kawo ɓata-gari cikin unguwa da kuma iƙirarin cewa ita ce shugaban karuwai da ƴan kwalta.
Batun kamawa da tura fitacciyar ƴar tiktok ɗin zuwa gidan yari ya ja hankalin al'ummar a jihar ta Kano.
Haka nan labarin fitar da ita daga inda kotu ta tura ta, wato gidan gyaran hali shi ma ya janyo muhawara mai zafi a jihar.
A ranar Litinin gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ba ta da hannu a sakin ƴar tiktok ɗin daga gidan yari bayan umarnin da kotu ta bayar na tsare ta.
managarciya Oct 30, 2021 12 169
managarciya Feb 3, 2025 3 110
Maryamah Dec 14, 2021 2 87
Maryamah Dec 16, 2021 10 73
managarciya Jun 24, 2023 5 73
managarciya Nov 13, 2023 0 550
managarciya Nov 12, 2023 0 346
managarciya Nov 12, 2023 0 335
managarciya Nov 12, 2023 0 416
managarciya Nov 11, 2023 1 702
managarciya Nov 23, 2021 0 464
"Cibiyar ta yi rijistar mata kusan 400 ana koyar da matan dunki da yin kayan kamshi...
managarciya Oct 15, 2021 0 372
tabbas in mun tafi majalisa sai mun kalubalanci duk wata doka da ta zama karfen...
managarciya Jan 1, 2025 0 207
managarciya Aug 19, 2021 0 601
managarciya Mar 3, 2024 0 298