Wata kotun majistare da ke Nomansland a karamar hukumar Fagge, jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare direban matar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, tare da wasu mutum biyu bisa zargin satar wayar matar sarkin, da kudade da wasu kayayyaki.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wadanda ake tuhuma sun hada da Sulaiman Yakubu Kulkude, Idris Musa da Abdullahi Usaini, inda aka gurfanar da su kan tuhume-tuhume uku da suka hada da hadin baki, sata da karbar kayan sata.
Alkalin kotun, Mai shari’a Halilu Abdurahman, ya amince da bayar da beli ga wadanda ake tuhuma tare kuma da dage shari’ar zuwa ranar 14 ga Afrilu, sai dai za a ci gaba da tsare su har sai sun cika sharuddan belin.






