Kotu Ta  Tasa Kwamishinan Zamfara  Zuwa Gida Gyaran Hali 

Kotu Ta  Tasa Kwamishinan Zamfara  Zuwa Gida Gyaran Hali 

 

Babbar Kotun jihar Zamfara mai zama a Gusau, a ranar Litinin ta garƙame kwamishinan noma da albarkatun ƙasa na jihar, Alhaji Ibrahim Magayaki, bisa rashin ɗa'a ga Kotu. 

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Alkalin Kotun mai shari'a Bello Shinkafi ya ba da umarnin a iza ƙeyar kwamishinan zuwa gidan Gyaran hali da ke garin Gusau. 
Alkalin yace Kotu ta dogara da tanadin sashi na 9 na kundin dokokin Fenal Code biyo bayan matakin kwanishinan na ƙin biyayya ga umarnin Kotu. 
Mai Shari'a Shinkafi yace Kwamishinan ya raina umarnin da Kotu ta bayar a shari'ar da ta gudana tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da kamfanin Dumbulum Investment. 
A cewar Alƙalin, Dumbulum Investement sun samu sahalewar Kotu na haɗa wa da wasu kadarorin gwamnati cikinsu har da manyan Motoci. Shinkafi ya bayyana ceqa duk da haka Kwamishinan Noma ya sa ƙafa ya shure umarnin kana ya sayar da wasu sassan Motocin waɗanda suna daga cikin waɗanda umarnin Kotu ya shafa.