Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar ‘Yan Majalisar Tarayya 4 Na PDP a Sokoto
Kotun daukaka kara dake zama a Abuja ta tabbatar da nasarar ‘yan majalisar wakillai 4 da suka fito daga jam’iyar PDP a jihar Sakkwato.
Jam’iyar PDP ta taya murna ga ‘yan majalisar kan nasarar da suka samu a kotun daukaka kara in da ta roke su da su cigaba da aiki tukuru domin samun nasarar jam’iyar a fannoni daban-daban.
'Yan majalisar da suka samu nasara sun hada da Honarabul Mani Maishinko Katami, mai wakiltar kananan hukumomin Binji da Silame da Honarabul Abdussamad Dasuki a Kebbe da Tambuwal da Honarabul Sa'idu Bargaja a Isa da Sabon-Birni da Honaraul Bashir Mohammed Gorau a Goronyo da Gada.
A sanarwar da jami'in yada labarai na PDP a jiha Hassan Sahabi Sanyinnawal ya fitar ya taya murna ga wadan da suka samu nasara da jam'iyar PDP gaba daya.
managarciya