Home Labarai Kotu ta soke zaɓen ɗan takarar majalisar waƙillai a Kebbi, ta kuma...

Kotu ta soke zaɓen ɗan takarar majalisar waƙillai a Kebbi, ta kuma ba da sabon umarni

15
0

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Birnin Kebbi ta soke zaɓen fidda gwani na mazabar wakilcin Argungu/Augie a Majalisar Wakilan Tarayya, tare da umartar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ta sake gudanar da sabon zaɓen cikin makonni biyu.

Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da Samir Salihu Felande ya shigar, inda ya ƙalubalanci ayyana Umar Hassan Augie a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar, yana mai cewa ba a gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani ba.

A hukuncin da ta yanke ranar Laraba, kotun ta umarci APC da ta shirya sabon zaɓen fidda gwani cikin wa’adin makonni biyu da aka kayyade, domin tantance ɗan takarar da zai wakilci jam’iyyar a wannan mazaba.

Wannan hukunci ya zama wani muhimmin ci gaba a takaddamar shari’a da ta dabaibaye tsarin zaɓen ɗan takarar jam’iyyar APC a mazabar Argungu/Augie ta Majalisar Wakilan Tarayya.

Hukuncin ya kuma sanya APC a ƙarƙashin wa’adin da kotu ta gindaya, inda aka wajabta mata gudanar da sabon zaɓen fidda gwani bisa umarnin kotun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here