Kotu ta soke babban taron PDP wanda aka zaɓi Tanimu Turaki a matsayin shugaban jam’iyyar
Babbar kotun tarayya da ke Ibadan ta soke babban taron jam’iyyar PDP da aka gudanar a ranar 15 ga Nuwamba, 2025 a jihar Oyo, inda aka zaɓi Tanimu Turaki a matsayin shugaban jam’iyyar.
Kotun ta kuma haramtawa Turaki da wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar ci gaba da bayyana kansu a matsayin shugabanni na PDP a matakin kasa.
A hukuncin da kotun ta yanke, an tabbatar da cewa kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar, wanda Sanata Samuel Anyanwu ke jagoranta, shi ne kadai halastaccen kwamitin gudanarwa na PDP, har sai an gudanar da babban taron kasa da doka ta amince da shi.





