Kotu ta saki wani magini da ake zargi da fyaɗe da kuma garkuwa da ƴar shekara 12

Kotu ta saki wani magini da ake zargi da fyaɗe da kuma garkuwa da ƴar shekara 12

A jiya Litinin ne wata kotun sauraron ƙararrakin fyade da rigingimun ma'aurata da ke Ikeja, jihar Legas, ta wanke da kuma sakin wani magini, Godspower Iporu da ake zargi da aikata laifin sace tare da lalata da ƴar makwabcinsa ƴar shekara 12 da haihuwa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya bayar da rahoton cewa, Mai shari’a Abiola Soladoye ta ce masu gabatar da kara sun gaza kawo sahihan hujjoji kan tuhume-tuhume biyu na lalata da yaro da kuma garkuwa daga hannun iyaye kan Iporu.

Ms Soladoye ta ce masu gabatar da kara, wato Gwamnatin Jihar Legas ta kasa gabatar da wacce lamarin ya faru a kan ta, inda ta ce ita ce ta kamata ta zama mai bada shaida lamba ɗaya a kan abinda ya faru.

A cewarta, wacce ake zargin laifin ya faru a kan ta, ya kamata ta kasance a gaban kotu don ba da shaida.

Ta ce: “Dukkanin shaidun da aka gabatar a gaban kotun, na baka da na takarda, komai kyawun da aka gabatar, ba za su iya kai ga yanke wa wanda ake kara hukunci ba, in babu shaidar wacce abun ya faru a kanta kan ko an sace ta daga hannun iyayenta ko kuma ba a sace ta ba.

“Shaidar wacce ake zargin laifin ya faru a kanta  na da matukar muhimmanci domin shaidarta za ta tabbatar da shaidar sauran shaidun masu gabatar da kara.

"Ba a sami wanda ake tuhuma da laifin tuhume-tuhume biyu ba, kuma kotu ta sallame shi kuma an wanke shi."