Kotu ta kori karar kalubalantar sauya Shekar gwamnan Zamfara zuwa APC

Kotu ta kori karar kalubalantar sauya Shekar gwamnan Zamfara zuwa APC

 
 Daga Hussaini Ibrahim.
 
 Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Gusau a jihar Zamfara ta kori karar da ke kalubalantar sauya shekar Gwamna Bello Matawalle, zuwa jam'iyyar APC daga Jamiyyar PDP.
 

 Kotun ta kuma bayar da umarnin biyan wadanda ake Kara naira N1m da masu shigar da kara su biya kowane daya daga cikin wadanda ake kara Sabo da bata masu lokacin da su kayi na zuwa Kotun.
 
 Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Aminu Bappah Aliyu, ya ce kotun ba ta da hurumin sauraren karar.
 
 Mai shari’a Bappa, ya ce asalin koken da masu shigar da kara suka shigar ba shi da wani inganci.

 
  "Ya kuma kara da cewa, kundin tsarin mulkin Nageriya ya ba kowane mutum Samar shiga kowace Jamiyyar da ya ke bukata. dan haka canza shekar gwamna Matawalle zuwa wata Jamiyya zai tafi da mukamin da yake Akai.
 
 Mai Sharia Aliyu yace ,"Yan majalisin Dokokin na Jiha ne kadai ke iya korar gwamna a bisa mukamin sa.</div