Kotu Ta Ki Aminta Da Rokon Shaikh Abduljabar Kabara 

Kotu Ta Ki Aminta Da Rokon Shaikh Abduljabar Kabara 

Lauyan Abduljabbar Kabara Barista Dalhatu Shehu Usman ya nemi Babbar Kotun Shariar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a Jihar Kano da ta dawo da shaidun masu gabatar da kara na 1 da na 2 da na 3 su zo kotu don su zame musu shaidun kariya a shariar da ake yi wa Abduljabbar Kabara. 

Haka kuma Barista Dalhatu Usman ya yi roko ga kotun zai sake yi wa wanda ake tuhuma tambayoyi. 
Sai dai masu gabatar da kara karkadhin jagorancin Barista Suraj Saida (SAN) sun yi suka game da wadannan roko na wadanda ake kara inda suka ce sake yi wa wanda ake tuhuma tambayoyi dal lauyansa yake so ya yi a karo na biyu. kawo tsaiko ne ga  shariar. 
Haka kuma sun ce ba  daidai ba ne shaidunsu su zo su bayar da kariya ko goyon baya ga wanda  tunda farko suka bayar da shaida akan cewa ya aikata laifin da ake tuhumarsa da shi don haka suka nemi kotu ta yi watsi da wannan roko na lauyan kariya. 
Kotun karkashin jagorancin Mai sharia Ibrahim Sarki Yola ta amince da bukatar Lauyan Abduljabbar ta sake yi wa Abduljabbar din tambayoyi. Sai dai ta ce za ta bayyana matsayinta a zama na gaba akan rokon neman yiyuwar dawowar shaidun masu gabatar da kara don su ba wa wanda ake kara kariya a karo na biyu. 
Tunda farko kuma  Lauyan Abduljabbar Kabara Barista Dalhatu Usman ya sake neman kotun da ta mayar da shariar zuwa wata kotun ta daban sakamakon zargin da suke yi cewa Alkalin ba zai yi adalci a shariar ba laakari da alakar da ke tsakaminsa da Shaikh Qaribullah Nasiru Kabara  wanda a cewarsa babban makiyi ne ga wanda ake kara. 
Akan wannan roko ma masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Suraj Saida (SAN) sun yi suka game da rokon na lauyan wanda ake kara inda suka kafa hujja da wasu shariu da suka gudana a manyan kotuna wanda suka nuna cewa ba  a canza kotu ba tare da wasu kwararan dalilai ba. 
Sai dai Barista Dalhatu  ya dage cewar idan har an zargi Alkali da rashin adalci to wajibi ne ya mayar da shariar wata kotun don tabbatar da adalci domin adalci a sharia ya fi komai. 
"Idan ana zargin alkali da alaka da mai kara ko mai gabatar da kara ko abin da ake sharia akansa to dole ya haramtawa kansa wannan shariar domin ya sabawa tsarin samar da adalci. Idan kuma bai yi ba to ya tabbatar da zargin da kansa"
Sai dai kotun ta yi watsi da wannan rokon na Lauyan Abduljabbar inda Alkalin kotun Mai sharia Ibrahim Sarki Yola ya kafa hujja da sashe na 196 (a, b)) na kundin dokar Laifuka ta ACJL ta Jihar Kano (2019) inda ya ce sashen ya nuna ana so wurin da za a yi sharia ya zama mafi dacewa kuma mafi kusa ga wanda ake kara 
"Idan aka yi laakari da wannan doka to wannan kotun ta fi kowacce kotu a Kano dacewa da yin wannan sharia saboda girman matsayinta da kuma kusancinta ga mazauni da kuma gidan gyaran halin da wanda ake kara yake tsare"
Haka  kuma Alkalin ya shawarci wanda ake kara ya kai korafinsa na rashin adalcin da yake zargin Alkalin da shi zuwa gaba. 
Daga nan Alkalin ya umarci masu gabatar da kara da su ci gaba da yin tambayoyinsu ga wanda ake kara a matsayinsa na shaidar kariya na farko.
Bayan kammala tambayoyin ne Kotun ta dage zaman sauraren shariar zuwa ranar 11 ga watan Agusta, 2022.
Gwamnatin Jihar Kano ce dai ta gurfanar da Abduljabbar Kabara gaban kotun bisa zargin sa da laifin yin batanci ga Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Was) da kuma tayar da hankulan jama'a.