Kotu Ta Daure Wani Mutum Da Ya Saci Cingam A Abuja

Kotu Ta Daure Wani Mutum Da Ya Saci Cingam A Abuja

 

Wata kotu da ke zamanta a Karu a Abuja ta yanke wa wani mutum dan shekara 50 mai suna Adamu Habib hukuncin daurin watanni hudu a gidan yari bisa samunsa da laifin satar fakiti biyu na cingam.

 
Wanda aka yankewa hukuncin, wanda ke zaune a kauyen Garki, ya amsa laifin sata.
 
Da yake yanke hukunci a jiya Talata, 29 ga watan Nuwamba, 2022, alkalin kotun, Ishaq Hassan, ya baiwa wanda ake tuhuma zabin tarar N10,000 tare da gargade shi da ya daina aikata laifuka, kamar yadda NAN ta ruwaito.
 
Mista Hassan ya kuma umarci wanda aka yankewa hukuncin da ya biya N12,840 diyya.
 
Lauyan masu shigar da kara, Olarewaju Osho, ya shaida wa kotun cewa wanda ya shigar da kara, Joseph Sunday na Faxx Supermarket, Abuja, ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Durumi a ranar 7 ga watan Nuwamba.
 
Mista Osho ya ce a ranar 18 ga watan Oktoba, wanda aka yanke wa hukuncin ya saci fakiti biyu na “Orbit” danko, wanda kudinsu ya kai N12,840.
 
Ya ce a lokacin da ‘yan sanda ke gudanar da bincike akai-akai, wanda ake tuhumar ya amince da aikata laifin.
 
Laifin a cewarsa ya sabawa tanadin sashe na 287 na kundin laifuffuka.