Kotu ta daure matashi kan zargin  ɓatanci ga Gwamna da matarsa a Sakkwato

Kotu ta daure matashi kan zargin  ɓatanci ga Gwamna da matarsa a Sakkwato
Kotun majistare ta daya ta bayar da umarnin a cigaba da tsare matashi Shafi'u Umar Tureta dan Shekara 36 har zuwa 6 ga watan Satumba 2024, domin fara sauraren karar da ake yi masa kan zargin batanci ga Gwamna Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu da matarsa Hajiya Fatima Ahmad Aliyu.

Alkalin  Kotun Majistare ta daya Fati Hassan ta bayar da umarnin a lokacin da take yanke hukuncin a ofishinta dake harabar kotun a Sakkwato. 


Barista Almustapha Yusuf Abubakar amadadin wanda ake  ƙara ya ce laifin da ake tuhuma lamari ne da ake bayar da beli kansa don haka bayan sun ji tuhumar da ake yi suke son samun damar da za su karbi wanda ake tuhuma kafin ranar da Alkali ya aiyana a dawo don soma sauraren kara.
Lauyan ya ce bayan an karanto tuhumar wanda ake zargi ya musanta ya aikata laifin.
Dan sanda Insfekta  Abdurrahman Mansur shi ne dan sandan da ya gabatar da wanda ake tuhuma tare da karanto  tuhumar da ake yi  guda biyu, da suka sabawa dokar jihar Sakkwato a daftarin na 2019 sashe na 378 da 379, "ka saɓa doka in da kai Shafi'u Umar dake zaune a unguwar Mabera ka tura wani bidiyo a ranar 18/7/2023 na matar gwamnan Sakkwato Hajiya Fatima Ahmad Aliyu tana bukin murnar ranar haihuwar ta, ka yi maganar karya kanta na cewa tana kari da almubazaranci a lokacin da talakawa ke cikin yunwa da damuwa."
A tuhumar da ake yi masa na laifi na biyu ya ce "sanya sakamakon jarabawar Gwamna Dakta Ahmad Aliyu na kammala sikandare da matakin F9 ka kira shi da bakauye, wanda bai iya magana da Turanci, hakan ɓata suna ne, hakan ya sa ake tuhumarka da aikata laifi.
Sakataren yada labarai na PDP Hassan Sahabi Sanyinnawal ya yi kira ga gwamnatin Sakkwato da ta saki matashin domin bai aikata laifi ba wannan abu ne dake nuna bita da kullin siyasa wanda ba za su lamunce hakan ba.
Ya ce kan bidiyon matar gwamna ai masoyanta ne,  suka fitar da lamarin  kowa ya gani suna buki ana yi mata karin kudi Naira da dala,  su ba su yi laifi ba, sai wanda ya yada, kuma sanda aka yi bukin talaka baya cikin yunwa ne?