Korarrun ma'aikatan CBN sun maka bankin a kotu

Korarrun ma'aikatan CBN sun maka bankin a kotu
 
Tsoffin ma’aikatan babban bankin Najeriya (CBN) da aka kora daga aiki a bara, sun maka babban bankin kasar a kotu.
 
A wata takardar kotu da TheCable ta gani a yau Litinin, ma’aikatan sun yi zargin cewa CBN ya sabawa manufofin cikin gida da dokokin kwadagon Najeriya, da kuma hakkokinsu da kuma hakkokin ma'aikata.
 
Masu ƙarar, wadanda Stephen Gana da wasu 32 suka wakilta, sun shigar da karar ne a gaban kotun ma'aikata ta kasa (NICN), Abuja.
 
Sun ce tsarin korar ta su, wanda aka yi shi a rubuce, mai kwanan watan 5 ga watan, 2024, ya sabawa ka’idojin da tsarin daukar ma'aikata ya tanadar bisa sashe na 36 na kundin tsarin mulkin Najeriya.
 
Masu ƙarar sun ce ba a yi amfani da tsarin tuntuba  da kuma sauraren shari'ar da doka ta tanadar ba.