Kisan Sarkin Gobir: Tinubu ya yi alwashin ɗaukar mataki

Kisan Sarkin Gobir: Tinubu ya yi alwashin ɗaukar mataki

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yi alla-wadai da kisan sarkin Gobir na Gatawa, Alhaji Isa Bawa, kuma ya sha alwashin ɗaukar matakan magance matsalar tsaro a ƙasar.

Shugaban ya yi wannan ta'aziyya ne a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan yaɗa labaru, Ajuri Ngelale.

Sanarwar ta ce: "Shugaba Bola Tinubu ya yi alla-wadai da abubuwan da suka faru waɗanda suka kai ga kisan Sarki Alhaji Isa Bawa.

Shugaban ya kuma bayyana cewa wajibi ne a hukunta waɗanda ke da hannu a lamarin.