Kisan Musulmi A Kaduna: Arewa Na Cikin Tasku Da Barazana Daban-Daban---Bafarawa

Kisan Musulmi A Kaduna: Arewa Na Cikin Tasku Da Barazana Daban-Daban---Bafarawa

Tsohon gwamnan jahar Sokoto, Attahiru Bafarawa ya baiyana alhininsa da kaduwa akan kisan gillar da aka yiwa wasu Musulmi dake gudanar da bikin Maulud a Kaduna sakamakon harin bam na jirgin soja a shekaranjiya.

Tsohon gwamna Bafarawa yace, hakika wannan kaskancin da sauran masifun dake fadawa arewa suna da muni da tausayi ga dukkan mai hankali.

Hakan yana kara nuna bukatar dole a nemi mafita da hada kai ga lamuran da yankin Arewa yake fuskanta.

Yana da kyau al'umma da shugabanin a yankin nan dasu dawo bisa hanyar gyara makoma al'umma don kuwa mun shiga cikin tasku da barazana iri daban daban a kasarmu ta haihuwa.

Yayi mamakin ganin duk da wadanan masifun na tashin hankali, boko Haram, ta'addanci da talauci da yunwa da Arewa ta samu kanta, har yanzu muna jiran wasu daga ketare dasu zo suyi mana gyara ko ceto mu akan wannan matsalolin.

Ya baiyana rashin mutunta juna, tarbiyya, hadin kai, tare da hassada da ko oho na kulawa da shugabani keyi mussaman dattawa a arewa ne a matsayin dalilan yawaitar wadanan matsalolin da kisan gilla dabam dabam dake fadawa al'ummar yankin Arewa.

Bafarawa ya nemi rundunar sojoji Najeriya da masu rike da mukaman tsaro dasu aiwatar da bincike a nan take, don hukunta duk wanda yake da hannu a wannan ganganci don daukar matakai na hana aukuwar irin haka anan gaba.

Ya jajjanta ma gwamnatin Kaduna, yan uwan da iyalan da abin ya shafa tare da neman al'umma dasu mayar da faruwa wannan lamarin a matsayin jarrabawa don samun sauki ga makoma ga wadanda bala'in da ya shafa da masu jinya a sanadiyar wannan mummunan harin.

Bafarawa ya bukaci Shugaban kasa Bola Tinubu da ya umurci rundunar soja dake da alhakin wannan aika-aika data gaggauta biyan diya da sake matsuguni ga wadanda bala'in ya afkawa dasu da iyalansu.