Kebbi: 'Yan Hisbah Sun Kama Samari da Yan Mata Suna Holewa a Hotel 

Kebbi: 'Yan Hisbah Sun Kama Samari da Yan Mata Suna Holewa a Hotel 

Jami'an rundunar 'yan Hisbah a jihar Kebbi sun kama yara matasa maza da mata 12 suna aikata baɗala a wani Hotel cikin birnin Kebbi, babban birnin jihar, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kwamandan rundunar 'yan sandan Musulunci watau Hisbah na Kebbi, Ustaz Suleiman Muhammad, shi ne ya tabbatar da haka yayin zantawa da yan jarida ranar Alhamis a Birnin Kebbi. 

Kwamandan ya ce matasan da aka kama da zargin aikata rashin ɗa'a a Otal ɗin sun kunshi maza Takwas da mata Huɗu kuma dukkansu sun amsa aikata laifin ba tare da gardama ba. 
Rundunar Hisbah ta gargaɗi masu Hotel da su guji baiwa yara maza da mata waɗanda shekarunsu ba su kai ba wurare don aikata alfasha da baɗala. 
Bayan haka Hisbah ta ƙara gargaɗi da babbar murya da matasan da ta kama da su guji fita shaƙatawa ba tare da izinin iyayensu ba. Bugu da kari, rundunar yan sandan Musuluncin ta shawarci iyaye da su kara sanya ido kan 'ya'yansu da waɗanda ke zama a karkashin kulawarsu, su san duk inda zasu je a ko wane lokaci.