Kebbi PDP ta goyi bayan haɗaka don kayar da APC a 2027

Kebbi PDP ta goyi bayan haɗaka don kayar da APC a 2027
 
 
Jam'iyar PDP a jihar Kebbi ta nuna goyon bayan ta ga shiga cikin hadaka don ganin an kawar da jam'iyyar APC a zaben 2027 a matakin jiha da kasar Nijeriya.
 
Bayyana wannan matsaya ta faru ne a ranar Assabar a Birnin Kebbi a karshen taron masu ruwa da tsaki da jam'iyar ta gudanar, kuma magoya bayan sun nuna bukatar warware rikicin cikin gida da PDP ke fama da shi.
 
A lokacin da yake magana da manema labarai jigo a PDP Ibrahim Mera ya bayyana cewa a matakin jiha sun amince za su yi aiki tukuru don ganin duk wata hadaka ta yi tasiri da za ta kawo karshen mulkin APC.
 
"Mun amince a gudanar da zaben shugabannin jamiya a jiha, a duk sanda jami'ya matakin kasa suka amince da a gudanar da shi",  a cewarsa.
 
Ya kara tabbatar da shugabanni za su yi tsayin daka don samar da goyon baya ga jami'ya a matakin jihar Kebbi.

Haka shugaban jam'iyyar a Kebbi Usman Suru ya baiwa mutanen jiha hakuri kan halin matsi da ake ciki ya yi masu albishir samun makoma mai kyau a gaba cikin rayuwa.

Tsohon dan takarar gwamna a 2023 a Janaral Aminu Bande ya soki matsalar tattalin arziki da ake fama da shi a jiha da kasa baki daya.

Ya kuma yi tir da halin gwamnatin APC a Kebbi kan musgunawa 'yan adawa da kama su da tsare su ba da hakki ba.

"Zan goyi bayan PDP a kowane shiri za ta yi don ganin an kawar da APC an kawo mulkin adalci a jihar Kebbi da Kasa baki daya," in ji Janaral Bande.