Kebbi: Gwamna Ya Dakatar da Malamin Musulunci a Mukami kan Maganar Luwadi 

Kebbi: Gwamna Ya Dakatar da Malamin Musulunci a Mukami kan Maganar Luwadi 
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya dakatar da babban sakataren na ofishin majalisar zartarwa. 
Gwamnan ya dauki matakin ne kan Nasiru Abubakar Kigo, saboda wata magana da ya yi game da luwadi da madigo a jihohin Kebbi da Sokoto. 
An tabbatar da dakatarwar ne a ranar Juma’a a cikin wata sanarwa da Vanguard ta samu ta bakin mai magana da yawun gwamnan, Ahmed Idris. 
Hakan na zuwa ne bayan Gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da daukar sababbin malamai 2,000 domin inganta harkar ilimi da ilimantarwa. 
Kwamishinar ilimi ta jihar, Dr. Halima Muhammad-Bande, ta ce an riga an tantance malamai 391 da suka cancanta a matakin farko. An samu jimillar masu neman aiki 18,000, amma 4,000 ne kawai aka tantance, inda sauran jerin sunayen za su fito nan gaba. 
Nasiru Kigo ya ce Kebbi da Sokoto su ne ke da mafi yawan 'yan luwadi da madigo da aka yi musu rajista, wanda wannan magana ta jawo maganganu. 
A cewarsa, an mika masa wasikar dakatarwa daga shugaban ma’aikata na jihar, Malami Shekare, bisa dokar aikin gwamnati. 
“Dangane da dokokin aikin gwamnati, an dakatar da kai har sai an kammala bincike kan wannan ikirari naka.” 
“Maganarka ta sabawa dabi’u, kuma tana bata sunan jihar da aka san ta da tarbiyya da kima.” 
Gwamnatin Jihar Kebbi a baya-bayan nan ta fitar da wata sanarwa inda ta karyata ikirarin Kigo, tana cewa karya ce.
An bayyana cewa Kigo, wanda kuma malamin addinin Musulunci ne, ya fadi hakan ne a lokacin wata ganawa ta musamman. An gudanar da taron ne a lokacin azumin Ramadan a rukunin gidaje na Adamu Aliero da ke cikin Birnin Kebbi.