Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa hanya daya tilo da Nijeriya za ta bi domin shawo kan kalubalen da take fuskanta a halin yanzu ita ce kayar da Bola Ahmed Tinubu daga mulki a zaben 2027.
Da yake magana a wata hira da ya yi a Channels Television, kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya ce babban burin ADC shi ne kayar da shugaban kasar a zabe mai zuwa.





