Katsina tabi sahun jihar Zamfara an rufe layukkan waya a jihar

Katsina tabi sahun jihar Zamfara an rufe layukkan waya a jihar

Katsina tabi sahun jihar Zamfara an rufe layukkan waya a jihar

An katse layukkan sadarwa a jihar Katsina abin da ke nuna ba batun sadarwa a jihar kenan.

A kalla kananan hukumomi 13 ne lamarin ya shafa in da aka katse sadarwarsu gaba daya in da ake tsammanin wannan yana cikin aikin da sojoji ke yi na fatatakar maharan daji da suka addabi yankunan a Arewa maso Yamma.

Kananan hukumomin da lamarin ya shafa su ne Sabuwa, Faskari, Dandume, Batsari, Danmusa, Kankara, Jibiya, Safana, Dutsin-Ma da Kurfi dukkansu suna kan dajin  Ruggu  daya daga mabuyar maharan.

Sauran ukun sun hada da  Funtua, Bakori da Malumfashi.

Wannan ya zo bayan hukumar sadarwa ta kasa ta musanta zance za ta katse layukkan sadarwa a jihar Katsina.