Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sallar Juma’a tare da shugabannin darikar Tijjaniyya a Masallacin Aso Villa da ke Abuja a ranar Juma’a. Jagoran tawagar darikar Tijjaniyya, Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass, shi ne ya jagoranci tawagar, inda suka yi addu’o’in samun albarka, zaman lafiya, da ci gaban Najeriya.
Ma'aikatar yada labarai da wayar da kan al'umma ce ta wallafa yadda sallar ta gudana a fadar shugaban kasa a shafinta na Facebook.
Taron ya biyo bayan ziyarar da shugabannin Tijjaniyya suka kawo Najeriya domin bikin Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass wanda ya kasance cikin manyan jagororin Tijjaniyya.
Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass ya bayyana jin dadinsa kan yadda Shugaba Tinubu ke tafiyar da mulki, yana mai addu’ar Allah ya kara masa hikima da nasara. Khalifa Inyass, wanda shi ne ɗan fitaccen jagoran darikar Tijjaniyya ya bayyana cewa dalilin zuwansu Najeriya shi ne bikin Mauludin Inyass.
Premium Times ta rahoto cewa Khalifan ya ce taron ya kara karfafa hadin kai tsakanin mabiya darikar a Najeriya da ma duniya baki daya Ya kuma tabbatar wa shugaba Tinubu da cikakken goyon bayan al’ummar Musulmi, musamman mabiya darikar Tijjaniyya miliyan 400 da ke Najeriya, Afirka ta Yamma da sauran sassan duniya.