KASUPDA: Ta yabawa shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari
Daga Shu'aibu Ibrahim.
Hukumar tsara birane na jihar kaduna, (KASUPDA) karkashin jagorancin Alh Sama'ila Dikko ta yabawa shugaban karamar hukumar sabon Gari ,Injiya Muhammad Usman.
Yabon ya biyo bayan ziyarar bazata da shugaban hukumar tsara birane ta jihar kaduna,Alh Sama'ila Dikko ya kai sabuwar tashar motar sabon Gari da ke 'yankarfe a yau Asabar.
Sama'ila ya nuna gamsuwarsa ganin yadda aikin sabuwar tashar yake tafiya babu kama hannu yaro,musamman yadda ake aiki babu dare ba rana don ganin ansamu an kammala.
Shugaban ya kuma bada shawarwari musamman kan yadda yake ganin tashan ya kamata ya kasance, tare da jawo hankalin jama'a kan yadda zasu amfana da aikin idan an kammala anan gaba.
Ya kuma bukaci injiya Usman da ya kara daura dammara da kauda kai ga surutai ko zagi da za'a dinga yi, yace saboda duk harkar gyara ta gaji haka.
Da yake tufa albarkacin bakinsa ga wakilinmu ,injiya Muhammad Usman ya nuna farin cikinsa da wannan ziyarar, duk da cewa ba wannan wurin kadai shugaban hukumar ya ziyarta ba ,ya ce sun fito ne don zagaya ayyukan da gwamnatin jihar kaduna keyi.
managarciya