Kashe Ummita: Kotu Ta Yanke Hukuncin Kashe Dan China a Kano 

Kashe Ummita: Kotu Ta Yanke Hukuncin Kashe Dan China a Kano 
 

Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a titin Miller karkashin jagorancin Mai sharia Sanusi Ado Ma'aji ta yanke hukuncin a kashe dan China Mistake Geng Quarang.

Alkalin ya yanke  hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kisan buduwarsa  Ummulkusum Sani Buhari wadda aka fi sani da  Ummita.
Shari'ar ta dauki lokaci kafin yanke hukuncin da ake ganin shi ne daidai ga wanda ya aikata laifi irin nasa.