Kasashen Afrika Suna  Fuskantar Matsananciyar Yunwa Sakamakon Karancin Ruwan Sama Tsawon Shekaru 6 A Jere

Kasashen Afrika Suna  Fuskantar Matsananciyar Yunwa Sakamakon Karancin Ruwan Sama Tsawon Shekaru 6 A Jere
 

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

 

Saudiya ta kaiwa Somalia agajin gaggawa na ton 70 na abinci don magance yunwa kungiyar agaji ta sarki Salman a Saudi Arabia ta aike da agajin kayakin abincin da yawansu ya kai tan 70, 

 
Zuwa ga yakin Gersbali ba Somalia sakamakon tsanantar yunwa da ke da nasaba da karancin ruwan saman da ya hana harkokin noma tare da haddasa fari, 
 
Somalia na daga cikin kasashen Afrika da yanzu haka ke fuskantar matsananciyar yunwa sakamakon fari biyo bayan karancin zubar ruwan sama tsawon shekaru 6 a jere ,
 
A jiya alhamis ne kayakin abincin suka isa yanki na Gersbali inda ake da kaso mai yawa na yan gudun hijirar da suka yi kaura daga yankunansu saboda matsananciyar yunwa, 
 
Kamfanin dillancin labaran Saudi Arabia ya bayyana cewa iyalai dubu 6 ne yanzu haka suka amfana da agajin abincin,
 
Agajin abincin wani bangare ne na kokarin masarautar Saudi Arabia don samar sauki ga wadanda matsalar fari ta shafa a kasar ta Somalia, 
 
Wasu bayanai sun ce kungiyar agajin sarki Salman ta gudanar da aikin ginin rijiyoyin murtsatse da matsugunan wucin gadi baya ga kayakin agaji na lafiya ga dubunnan mutanen da fari ya koro daga yankunansu,