Kasafin kuɗi: Za a kashe wa Tinubu Da Shettima Naira biliyan 9.36 wajen tafiye-tafiye da ciye-ciye
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakin sa Kashim Shettima za su kashe Naira biliyan 9.36 wajen tafiye-tafiye da ciye-ciye.
DAILY TRUST ta rawaito cewa hakan na kunshe ne a daftarin kasafin kuɗi na 2025 da ma'aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta fitar.
A daftarin kasafin kudin, Tinubu zai kashe Naira biliyan 7.44 wajen tafiye-tafiye da ciye-ciye, inda shi kuma Shettima zai laƙume Naira biliyan 1.9.
A cewar Daily Trust, a tafiye-tafiye kawai, Tinubu zai kashe Naira biliyan 6.14, sannan ya laƙume Naira miliyan ɗari 431.6 a wajen ciye-ciye da abinci da ma kayan abincin a 2025.
Hazalika Shettima zai kashe Naira biliyan 1.31 wajen tafiye-tafiye na kasashen waje inda zai kashe Naira miliyan 417.5 wajen tafiye-tafiye a cikin gida Nijeriya, dukkan 2025.
managarciya