Karon farko bayan shekaru goma, Sanusi da Jonathan an gana a Abuja

Karon farko bayan shekaru goma, Sanusi da Jonathan an gana a Abuja

Karon farko bayan shekaru 10, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan sun hadu da Sarkin Kano, Dr. Khalifa Muhammadu Sanusi na II a yau Alhamis.

A shekarar 2014, Jonathan ya dakatar da tsohon Gwamnan na CBN bayan ya bayyana cewa Dala Biliyan 49.8 sun yi batan dabo a karkashin mulkin Jonathan.

Lamarin dai ya haifar da ce-ce-ku-ce a yayin da mutanen biyu suka gaza haduwa ido da ido.

Sai dai Jonathan da Sanusi sun gaisa a yayin bikin kaddamar da littafin da tsohon ministan kudi Shamsudeen Usman yayi wa gyara.

A cikin littafin, Sanusi ya bada shaida game da lamarin da ya sanya ya bar bankin na CBN.

Shima tsohon shugaban kasar da ya halarci taron, ya dau lokaci yana bayani kan musanta zargin cewa kudaden sun yi batan dabo a lokacin sa.

Anasa jawabin, Sanusi wanda shi ne bako na mussaman ya kira Jonathan da "Maigidana da ya kore ni" inda ya kara da cewa, "Nasan kowa na tsammanin zan mayar da martani, amma ba zan mayar da martani ba".