Karin Wahala Gaban 'Yan Nijeriya: Man Fetur Zai Zarce 540, Motoci Za Su Kara Tsada

Karin Wahala Gaban 'Yan Nijeriya: Man Fetur Zai Zarce 540, Motoci Za Su Kara Tsada

 

Alamu na nuna cewa farashin man fetur zai iya tashi a Najeriya a lokacin da mutane ba su gama farfadowa daga radadin cire tallafi ba. 

A makon nan Vanguard ta kawo labari cewa canjin da aka samu na farashin kudin kasar waje zai yi sanadiyyar da litan fetur zai kara tsada sosai. 
‘Yan kasuwa sun ce karyewar Naira na da tasiri a kasuwancinsu, farashin da su ke sayen man fetur zai karu, hakan zai canza farashi a gidajen mai. 
An tsaida farashin kowane lita a kusan N540 ne a lokacin da aka yi lissafin Dalar Amurka a tsohon farashi, kafin bankin CBN ya canza tsari. 
Bincike ya nunawa jaridar cewa mafi yawan masu sarin mai sun canza farashin litarsu zuwa tsakanin N492 da 495 daga N488 da aka saba. 
Idan aka leka gidajen mai a Legas, farashi ya fara tashi ya na komawa kimanin N515, a wajen garin kuwa akwai inda ake saida lita fiye da N650. 
Manyan dillalai sun ce tun da aka koma saida Dala a kan N770, ya zama dole farashin gidajen mai ya canza, lita za ta kai akalla N550. 
Rahoton ya ce ‘yan kasuwan da aka ba lasisi sun fita sayo man fetur yanzu a ketare. 
Saboda ganin sun samu riba, kamfanonin su na hada-kai da bankuna domin samun kudin kasashen waje da ake amfani da su wajen ciniki a ketare. 
Wasu shugabannin kamfanonin mai da aka yi hira da su, sun shaida cewa za a dauki akalla daga yanzu zuwa Yuli kafin man su ya shigo Najeriya. 
Ganin yadda farashi yake canzawa a kasuwa, shugaban DAPPMAN, Olufemi Adewole ya ce ba a tilasta masu saida mai a wani kayadajjen farashi ba. 
Ana haka ne Punch ta ce karyewar Nairan zai jawo motoci su kara tsada a Najeriya domin kudin shigo da su daga ketare zai karu da kimanin 40%. 
Hakan ya na zuwa ne bayan an ji labari watakila daga yanzu motoci za su rika barkowa Najeriya daga kasashen waje kamar yadda aka saba a da. 
Hana shigo da motoci ta kasa ya jawo hukumar Kwastam ta ga kudin shiga da ake samu ya ja baya. Haka zalika tsarin bai yi wa 'yan kasuwa dadi ba.