Kada ku yi amfani da kuɗin fanshon ku wajen ƙara aure – Dikko Radda ya shawarci ƴan fansho a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya gargadi tsoffin ma’aikatan gwamnati da kada su yi amfani da kuɗaɗen fanshon su wajen ƙara auren sabuwar mata bayan ritaya, inda ya shawarce su da su yi amfani da kudinsu cikin hikima.
Ya yi wannan jawabi ne yayin kaddamar da rabon ₦41 biliyan na hakkokin tsoffin ma’aikata na jihar da kananan hukumomi.
Radda ya ce wasu tsoffin ma’aikata kan kashe kudinsu ba daidai ba bayan karɓar hakkokinsu, wanda ke jefa su cikin hali na rashin jin daɗi.
Ya bayyana cewa biyan hakkokin fansho ya kai jimillar ₦45.89 biliyan tun daga farko ga mutane 14,560.
Gwamnan ya sanar da sanya hannu kan sabuwar dokar fansho ta 2025 da kaddamar da hukumar fansho ta jihar Katsina da kwamitin sauya tsarin Fansho domin sa ido kan sabon tsarin.
Ya kuma tabbatar da cewa babu wani tsohon ma’aikaci da zai bar aiki ba tare da an biya masa hakkinsa ba.






