Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta bayyana cewa a watan Maris an siyar da gas mai girman 5kg kan kudi N6,591 bayan tashin farashin.
Wannan karin shi yake nuna an samu karin kaso 7.1% idan aka kwatanta da watan Faburairu da ake siyarwa N6,154.
Yayin da a cikin shekara farashin gas ya karu da kaso 42.9% idan aka kwatanta da N4,610 a watan Maris na shekarar 2024.
Ana amfani da wannan gas ne wajen yin girki da wasu aikace-aikace a gidaje.
Jihohin da ke sayan gas da tsada (5kg)
1. Kano: N7,609.00
2. Ogun: N7,363.64
3. Akwa Ibom: N7,162.50
4.. Sokoto: 6,500
Jihohin da ke sayan gas da sauki (5kg)
1. Adamawa: N5,312.50
2.Taraba: N5,375.00
3. Zamfara: N5,550.00
Gas: Nawa ake sayen tulun kilo 12?
Har ila yau, NBS ta ce ‘yan Najeriya na biyan N15,929 kan gas mai girman 12kg a watan Maris da ta gabata. Hakan ya nuna an samu karin kaso 5.7 idan aka kwatanta da watan Faburairu kan N15,060, cewar The Guardian.
Yayin da a cikin shekara farashin ya karu da kaso 55.2% idan aka kwatanta da farkon shekarar bara.





