Home Finafinnai Kannywood: Jarumar Finafinnan Hausa ta fadi dalilin daina harkar

Kannywood: Jarumar Finafinnan Hausa ta fadi dalilin daina harkar

2
0

Jarumar masana’antar Kannywood, Hassana Ibrahim Rano wadda aka fi sani da Safiyya Zabi Biyu, ta sanar da cewa ta yanke shawarar yin ritaya daga harkar shirya fina-finai.

Jarumar ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram, inda ta gode wa masoyan ta da duk wanda ya ba ta goyon baya tun lokacin da take cikin harkar fim.

Wannan sanarwa ta zo ne kwanaki kadan bayan mahaifiyarta ta fito fili ta bayyana cewa ba da yardarta ake barin ‘yarta ta ci gaba da yin fim ba.

Lamarin ya jawo cece-kuce a tsakanin masoya da mabiyan harkar fina-finan Hausa, inda da dama suka rika jiran matakin da jarumar za ta dauka.

A cikin sakon nata, Hassana Ibrahim Rano ta ce tana matukar godiya da damar da aka ba ta da kuma addu’o’in da ta samu daga masoya.

Ta kuma yi addu’ar Allah ya saka wa kowa da alheri tare da ci gaba da zama karfin su, yayin da ta rufe sakon da kalmar godiya ga duk wadanda suka mara mata baya a tsawon lokacin da ta shafe a masana’antar Kannywood.

Dalilin daina harkar fim ya faru ne kan wani abu da ta bar shi cikin zuciyarta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here