Kananan Hukumomi 40 a Najeriya da Wuya a Yi Zabe  a 2023

Kananan Hukumomi 40 a Najeriya da Wuya a Yi Zabe  a 2023

 

Ta'azzarar rashin tsaro a Najeriya ya sa 'yan kasar da dama cikin tashin hankali, kuma kullum tsoro karuwa yake a zukatan wasu da dama. Jaridar Punch, ta ruwaito cewa, akwai kananan hukumo sama da 40 da ba lallai su kada kuri'u ba a zabe mai zuwa saboda yawaitar harin 'yan ta'adda.

Kananan hukumomin 40 suna karkashin fadin jihohin Kaduna, Zamfara, Niger, Katsina, Abia da Imo ne, kuma ga su kamar haka: 'Yan bindiga sun mamaye kananan hukumomi 8 a Kaduna Chikun Kajuru Kachia Zangon Kataf Kauru Lare Birnin Gwari, Giwa.
 
'Yan ta'adda da 'yan bindiga sun karbe kananan hukumomi 9 a Zamfara Maru Tsafe Bakura Anka Maradun Gusau Bukkuyum Shinkafi Bungudu.
 
Boko Haram da sauran 'yan ta'adda sun kama kananan hukumomi 7 a Neja Rafi Munyan Shiroro Magama Mashegu Mariaga Wushishi.
 
Kananan hukumomi 11 cikin 23 na Sokoto na fama hare-hare Illela Rabbah Sabon-Birni Isa Wurno Gada Goronyo Tangaza Gudu Denge-Shuni Kebbe.
 
Kanan hukumo 5 da 'yan bindiga suka addaba a jihar Imo Orsu Orlu Oru East Oru West Njaba.