Home Daga Marubutanmu Kana Naka….:Fita Ta Bakwai

Kana Naka….:Fita Ta Bakwai

2
0

Janafty
KANA NAKA..!

Wattpad:JamilaUmar315
Mallakar:Janafty
Arewabook:Jamilaumarjanafty
Book 1

            🅿️07

Bayan ta gama fad’an rashin gayama Goggon karofi sai ta koma fad’an kayan da aka bani bayan tace na dauko mata ta gani Badariya karama ce acikin ya’yan mama ammh da ace itace Babba da abubuwa da dama sun gyaru tana da kyakyawan zuciya da Hali mai kyau.
Ina kallonta ta d’aga kayan a rene tana tabe baki kafin tace”Yanzu Anty Fa’iza abunda suka baki kenan acikin Uban kayan akwati goma da suka tafi kaiwa Abuja..?
Duk da ba duka naji mganar ta ba,ammh na dauki wasu,Sannan ina Bin bakin wanda na saba mgana dashi na kan Fahimci abunda yace ko da ban ji ba.
Ban ce mata komai ba sai ma wani mirmishin takaici da nayi,na sani ko Lokacin aurena ya ishaq bai min lefe ba ballatana yanzu ba da bani zai aura ba,Daman a wanchan Lokacin Baba ne ya matsa masa akan sai yayin lefe ba Sadaka ya aura masa ni ba, awanchan Lokacin Mama ta shiga mganar tayi ruwa tayi tsaki akan ita da kanta zata had’amin lefe nagani na Fad’a da ya kara tambayata sai tace tuni ta bama ya ishaq ya kaimun kaya ahalin kaya ko kala goma basu kai ba sannan saukakku dai ba masu tsada ba daman tun a baya na fada muku Baba shi ba magidanci ba ne mai bin diddigin abunda ke faruwa a cikin gidansa ba shiyasa wani Lokacin Mama kan yi nasara a kansa da kuma kila an yi masa surkullen mutanen yamai.
Ni ban damu ba saboda ba kayan ba ne a gabana, ko su bani ko kar su bani bazai kankare yadda bani da Daraja a idanuwan ya ishaq da su kansu ba.
Har ta gama fadan ta ban bude baki nayi mata mgana ba to me zan ce..?duk abunda zan ce alokacin bashi da amfani Saboda ajiyan agaban Mutane Anty Binta ta kara maimaita Dakyar ta lallaahi Ya ishaq ya amince ya siyamin ma kala ukun da aka bani Domin da farko cewa yayi bazai siya ba Saboda ko ya siya zai yi asara ne ban san Darajan su ba sai da tayi ta basa baki sannan ya amince to saboda mene zan damu..? Awannan gabar da auran mu ya zama jingina ba lalle ne Hakkokina su rataya a wuyansa ba ni ba Dolen sa ba ne yanzu Saboda haka raina ya daina Damuwa kan duk Tozarcin da zai aikata agareni.
Kuma na kudiri araina bazan saka kayan sa ba,Akallah dai zan fara Dogara ga kaina ko Saboda ya’yana na fara Tunanin zamana ahaka bazai yuyumin ba in ya’yansa Dolensa ne,ni na tashi adolensa bazan bar gidansa yanzu ba Saboda lokaci bai yi ba ya’ya na suna Bukata ta, sosai in na tafi na bar su basu da wanda zai kula da su da Tarbiyan su ina tsoron su tashi Cikin maraicin uwa kamar yadda muma muka tashi cikin wannan maraicin muna da uwa a raye ammh kamar bataa raye ne a wajenmu.
Tattara komai nayi na tusa cikin Wardrope d’ina ban kuma yarda nayi mganar da kowa ba Daman Ya Asiya ce kadai take kirana kan Sha’anin Bikin Yaya mariya ko sau d’aya bata kirani ba ita ta na da Zafi ne Ko zuwa tayi had’uwa goma sai sun yi Cacan baki da Anty binta gata irin tanada Sauri Saurin mgana ne kafin Anty Binta ta fadi daya ta maida mata Biyar Shiyasa bata cika zuwa katsina ba sai da Dalili mai girma waya kuma bamu cika mgana ba Saboda abu kad’an zataji ranta ke baci kuma bata da Hakuri ko kada’n.
Biki nata karatowa barayin su Mama suna ta shirin su gayya Mama tayi bani da Gayya ba Domin tace sai yanzu ta san Ishaq zai yi aure ni ina gida bansan halin da suke ciki ba,bani cikin kwanciyar Hankali Saboda ina ta mafarkin Tamadina sai na tsorta kada tazo ta mutu itama bamu gana ba sai na fara Tunanin ya kamata naje na gaisheta na Dubata Saboda mahaifiyata ce in na rasata a wannan gabar sai nafi kowa kuka Saboda dani kad’ai ne bata gana ba.
Na fara Tunanin Tafiya sai dai matsaalan kudi ne Dubu daya da Dari Biyar suka Ragemin a hannuna cikin Dubu biyar din da Ya Ishaq ya barmun da zai tafi sannan Tunda ya tafi ko sau daya bai kirani yaji Halin da muke ciki ni da yara ba nima kuma ban kirasa ba Sai dai na riga na kuduru niyyar zuwa gaida Tamadina Cikin Satin nan da zai shiga kafin Lokacin Bikin yazo.
Na shirya tafiya ta Ranar asabar in su Amir sun tafi Hadda,Shiyasa Ranar jumma’a da Daddare na yi ma Ya Ishaq flashing Saboda wayata ba kati na ma manta Rabon da na saka mata kati ba na kira daman sai dai mai son mgana dani ya kirani bansan adadin Flashing din da nayi masa bai kira ba sai chan naga kiransa na dauka jikina na rawa na saka ta a amsa kuwwa na kara kunne tun kafin nayi mgana ya Dakamin Tsawar da sai da tasa na razana Cikin Fadansa yace”Haba don Allah wai meye haka Fa’iza..? Sai flashing kike yi min tunda kika ga ban kira ba ai kinsan ina wani abu mai muhimmanci ne ko ina tare da wani mutum mai muhimmanci ke duk abunda kika fara Hankali bai isa ya baki ki bar shi haka ba..?
Sai naji kwallh ta ciko cikin kwarmin Idanuwa na cikin rawan zuciya da na Murya nace”Kayi..ka..yi hakuri..Ban..Sani ba ne..”
Karamin tsaki yaja kafin yace”Zan kiraki in na koma gida ina tare da Zeey ne..”
Daga haka ya katse wayarsa ina jin muryanta kafin ya katse tana fadin”Honey kai da waye kake ta Ihu haka..?kamar a kusa da wayar tayi mganar shiyasa na ji ta.
Ban ji me yace mata ba ya katse kiran sai na Sulale gefen gadona na fashe da kuka Allah yasa yaran duk sun kwanta har ta Ahmad yayi barci kuka nayi wanda naji ya isheni nasan bani da wata Daraja a idanuwan Ishaq ammh ban dauka har agaban wacce zai aura ma bani Daraja ba ,Sai na fara tunanin wani irin karb’a amaryan sa zatayi min in muka fara Had’uwa sannan me ya fada mata akaina..?
Wata zuciya ta amsamin ya fad’amata ke bakomai bace face bebiya mummuna baka mara gata sannan mara ilimin zamani wacce bata da komai atare da ita tuna haka yasa kuka na ya karu bansan tsawon Lokacin da na Dauka ina kukana ba sai da nagaji sannan na tashi na Shiga Tiolet na wanke fuska ta na fito na k’i yi barci ina jiran kiransa na riga na sakama raina Gobe zan je na Duba Tamadina kuma ba yadda zan iya tafiya batare da izininsa ba..
Bai kira ba sai wajen sha d’aya da Rabi na Dare sannan ya kirani ina D’auka fada ya hauni da shi wai ni bai san me nake yi ba sannan bani da Hankali komai ba cikin lissafi nake yi ba ni dai Hakuri nayi ta basa sai da ya sha iska ya gama wulakacin nasa sannan yace”Ina yara na..? Ina fatan suna nan cikin koshin lafiya ko..?
Nayi saurin amsa mai da suna lafiya jin nayi shuru yasa yace”Fa’iza fadi abunda yasa kika addabeni da Flashing ina da shiga office da Safe zan kwanta akan Lokaci”
Cikin yanayin mganata nace”Da dama..Ina so ne gobe naje Dutsenmah na Duba Tamadina”
Cewa yayi bai ji ba na sake bud’e muryanta na kara gayamai sai kawai yace”wacece haka..?
Ban yi mamaki sanin Waye Ya ishaq kai tsaye nace”Babarmu..”
Karamin Tsaki yaja kafin yace”Daman nasan bana ganin kiranki sai wata Bukatarki ta taso miki Fa’iza baki da wani Amfani sai kina da bukatar wani abu..me akayi da kike son ki tafi..?
Kai tsaye nace”Tayi rashin lafiya ne ni kad’ai ne ban je na Dubata ba”
Kyafci yayi kafin yace”Kada nace bazaki je ba kice na hanaki ganin mahaifiyarki Allah ya kiyaye hanya..Sai dai kada ki kuskura ki tafin min da yara na gidan da ba wanda yasan su, salon suje suna Rab’e rab’e ke kanki ai araben zaki je Ahmad na amince kawai ki tafi dashi Shima Saboda yana shan Nono ne”
Ban damu ba nace”Eh daman suna Hadda haruna in ya Dauko su in ban dawo ba gidan mama zan ce ya kai su”
Da Sauri ya tasomin yana fadin”Au Dare ma zaki kai?ko nufin ki Daman chan zaki kwana..?
Cikin daburcewa nace”A”a..Dama..Dama ina so na Biya Karofi na gaida Goggo ne”
Kai tsaye cikin D’agawar Harshe yace”Ban amince ba..Ban kuma baki izinina ba..Dutsemah kadai zaki je shima Dubiya ce in kika Kai dare Fa’iza wlh sai ranki ya baci..Wato ki je a had’u ayi ta gulmana ana zagina nan Goggon karofi ta kirani tana min Fad’a duk akan ki wai in nayi aure  kada na wulakantaki to in tana ganin ban taimake ki ba meyasa sanda Baba ya nuna zai Aura min ke bata famsheni ta aura miki Isa ba..?karewar tana kaunarki da Tausayin ba..bana son Rainin wayau kada ki sake naji kin taka Karofi in kuma naji wlh tallahi kin ji Rantsuwan musulmi Fa’iza zaki ga Other side of me da baki Taba gani ba..”
Hawaye wani na koran wani suke zuban min cikin wani yanayi nace”Ko gidan Ya..ya mariya..?
Dogon Tsaki yaja kafin yace”Ita kuma wannan na yi miki iyaka da ki kara Takawa gidanta tunda bata da mutumci bata da,kunya har ni nan zata rika gani na, tana min kallon banza kamar taga kashi..?,Sannan naji Labarin ta raina Mama ta kuma raina Anty Binta har sa’insa tana yi da ita in dai ni ke auran ki kin bar kara taka gidan da ake cin zarafin Uwa ta da yayata sannan itama ki gayamata kada ta kuskura na kara ganin kafarta agida na in kuma ta bari muka Hadu sai na Koreta wlh”
Daga haka kit ya kashe wayar sai nayi sororo da waya a Hannuna Hawayena suna D’iga a saman wayar gefen gado na koma na zauna kukana ya kasa Fitowa sai dai Hawayen kawai ina Tuna mganganunsa in ya zagi Yaya mariya bazan damu ba Tunda har Goggo bata tsira ba awajensa ni Ya ishaq daman ya saba kirana da duk sunan da yaga Dama,na yarda yace ban da amfani sannan bana Kiransa sai in ina da Bukata Saboda tun farkon fara aikinsa a abuja ina kiransa Ranar ya Dauka ya yi min  fata fata yana min ihu akan  me zan rika Damunsa na D’auka Abuja irin katsina ne..?
Abuja yana harka da Mutane Dabam Dabam bazai zo cikin jama’a yana wage baki da murya Saboda mgana dani ba kada na kara kiransa kada na kunyatasa watarana cikin jama’a Tunda ga ranar ban kara gigin kara kiransa ba kada na kunyatasa kamar yadda yace d’in sannan Halin ko in kula da ya nuna kan Tamadina bai Dameni ba Domin bashi ba ne na farko ba kuma Kila bazai zama na karshe ba.
Tunda ya ke aure na bai Taba taka gidan da Tamadina ke aure da,Niyyar gaida mahaifiyata ba akwai wani zuwan da mukayi karofi bayan Haihuwar Anum ne da Mama da shi a motar abokinsa Dakyar ya aminnce ya biya dani zan kai mata Anum saboda sanda aka haifeta bata zo ba Shima din Sai da na roki Mama ta saka baki ya Biya dani ammh K’iri k’iri yaki bari na shiga da Amir sannan Daga shi har Mama suka ki’ shiga Gidan suka tsaya a mota ni kuma ya bani Minti goma.
Ina shiga ko zama ban yi da kyau ba ya fara Hon ta na rike da Anum a hannunta ni na fad’amata tare da su Mama muke bata damu ba tayi Lullubi ta fito har kofar gida suka gaisa Ya ishaq kuma ki’ri kiri yak’i fitowa Daga mota Mama ce ma ta fito suka gaisa duk yadda Tamadina taso ta Dauki Amir ya ishaq ya ki fitowa da shi yana rike dashi,Sannan ya hanani komawa cikin gidan ko cikakken gaisuwa bamu yi da ita ba yace na shigo mota mu tafi da nace bamu gaisa ba sai yace sai dai ko na san yadda zan yi na Dawo gida wlh in ya tafi bazai dawo ya Daukeni ba.
Ina ji ina gani na shiga mota  bayan Tamadina ta bani Anum,Tana d’agamin hannun idanuwanta sun cika da kwallah,ni kaina kwallar ta kawo cikin Idanuwana da Dubara na share mun D’auki Hanya Ya Ishaq ya juyo yana fadin”Tab Mama ashe kice Allah ya Dubi Fa’iza da idon Rahma ana jin mganarta har ana gane me take fad’i naji Babarsu ba’a ko jin abunda take fadi sai uban Ihu kawai ake ji tana yi”
Da Dauri na Dago ina kallonsa shi kuma ko ajikinsa maimakon Mama ta kwab’amai a’a sai cewa ma tayi”Eh mana ai uwar su ce ainihin Bebiyan Sai dai kaji tashin Ihu nan kuma wai mgana take yi”
Ya Ishaq yayi dariya yana kallona kafin yace”Allah ya taimake ki Fa’iza da yanzu kema ihun kawai zamu rika ji”
Daga shi har Mama Dariya suka saka har muka iso gida ina kuka Tozarcin ya tashi daga kaina da yan’uwa ya koma Har kan mahaifiyata shiyasa abunda yayi yau ba zame min Sabo ba sai dai shi Tozarci baka Sabo da shi ko yau aka yi maka shi sai kaji ba Dad’i.
Ban karaya ba sannan na yi kudurin sai naje shiyasa da wuri na tashi na shirya yara suka tafi Hadda sannan na yi wanka na shirya Ahmad Na fara Tunanin me zan kai mata bani da komai ban ijiye ba sannan ban bama wani ajiya ba ina bakincikin wannan Rayuwar da nike ciki ko da bani da shi akwai Hakkin uwata a kaina sannan wazai amince bani da shi Tunda kowa yasan Ya Ishaq nada Rufin asiri sanna  ba kowa yasan yanayin Rariyar ba ballatana yasan yanayin zubar ruwanta ba Nasan Su Yaya mariya suna iya bakin kokarin su ammh suma ai ya’yanta ne kamar yadda nake yarta akwai Hakkin kyautata mata a wuyana.
Da na rasa abunda zan kai mata sai na D’ibar mata garin rogo wanda Ya Ishaq kan siya saboda yara in yaga Dama sannan shima yana son gari da siga,sabulin wankan mu ya kusa karewa sai na Dibar mata na wanki da na Klin,sai na Daukan mata Maltina guda hudu na kulle aleda ina da Burin ko kaya na bata ammh bani Dashi sannan bazan iya bama mahaifiyata tsohon kayana ba kamar na ci mata mutumci ne.
Sai nayi Hakuri na Dauki iya abunda nake da shi koda goma tayi na isa Dutsemah sai dai Tamadina ta ganni kamar Daga sama Allah Sarki Uwa bakinta yaki Rufuwa ta rasa ina zata sakani Saboda Murna taji Sauki Sai dai kafafun sun kumbura abokan zamanta sun ce Daga dare zuwa Safe ta tashi da Kafafu a kumbure ana ta dai shafa mganin sanyi.
Tunda muka zo ta kama Ahmad ta goya ram a bayanta sai kallonta nake yi farinciki ya cikani ta tambayi su Amir nace suna makaranta tace meyasa ban kawo su ta ga yadda suka kara girma ba..? Idona ya ciko da kwallah ya’ya na ne suma ammh bani da iko da su ballatana mahaifiyata tayi iko dasu suma dai  ce mata kawai nayi zan kawo su watarana.
Abokiyar zamanta Maman isuhu suke kiranta tayi danwake ta kawomin naci abuna muna ta Hira Da Tamadina duk da mganar nata sai a hankali ammh mu ya’yanta da ta zame mana Dole muna ganewa ni dai ban gayamata wani abu da zai tada mata Hankali ba ko mganar auran Ya ishaq ban mata karfe biyu nayi na tashi na fara shirin tafiya bayan nayi sallah na bata abunda nazo da shi ta Dafa kaina tana ta sakamin albarka.
Ta bani Ahmad na goya a baya na,na saka Hijabina nayi ma mutan gidan Sallama ta rakani har zaure tana D’ingisawa ina ta koma sai tace sai ta Rakani mun yi sallama kamar kar mu rabu har zan tafi ta riko Hannuna na Juyo ina kallonta ta kuramin ido sai naji jikina yayi sanyi cikin mamaki nace”Manene ke faruwa Tamadina..?
Kawai sai ta Dafa kaina ta jijjiga nata kafin tace”Kiii….yi….hakuri..Fa’iza..!
Sai naji raunina ya bayyana da Sauri na kauda kaina ina Boye hawaye na kafin na gyada kai ina fadin”In sha Allahu..Allah ya baki lafiya”
Daga haka muka yi sallama har na kule tana Dagamin Hannu.
Tunda bai amince na biya karofi ba Daganan ma hau motar katsina,na koma gida hud’u saura sallah kawai nayi na fara kokarin dora girki Saboda yan makaranta ammh gabadaya sai ina jin jikina duk yayi wani irin sanyi komai nawa yayi sanyi kamar an zare ma jikina lakka.
Ko su Amir da suka Dawo makaranta sai da suka ga yanayi na Amir mai wayon ciki ne ya dinga ce min”Baki da lafiya ne Umma..?
Sai nace mai a’a saboda kada na tayar musu da hankali sai na warware na shiga cikin su mukaci abinci bayan sun gama mukayi sallar isha’i tare bayan mun idar nayi musu karatun Qur’ani na kara ma kowannen su inda ya ke sannan nace su yi na makarantan bokon su da aka basu amatsayin aikin gida.


Tunda Ya ishaq ya tafi bai Dawo ba sai ana Saura kwana uku D’aurin auran sa,sannan ya Dawo shima din gidan Mama ya sauka sai Dare na gansa,gari kuma na wayewa ya kara fita Jamal ya Dawo tare naga suna ta zirga zirgan karbo dinkuna Gidan Mama kuma ya fara cika da baki Badariya ta fadamin Hajiyar Dala ta iso tun jiya sannan da yan’uwan Mama na yamai ni dai ta barayina bana wani shiri Saboda ban ga abunda zan shiryamawa ba.
Ana jibi Daurin aure da yammah sai ga Anty Mamah da Halisa sun zo gida na karb’e su hannun Biyu Saboda suna da kirki Har Halisa ba ta Dauko Halin Anty Binta ba.
Na kawo musu ruwa kenan na zauna muna gaisawa,ba islamiya Saboda alhamis ne Su Amir suna gidan Mama dazu da Jamal ya kawo wasu kayan Shahen Ya Ishaq ya tafi da su Ahmad ne kad’ai tare dani.
Bayan mun gaisa Anty Mamah ta kalleni sama da kasa har sai na Tsargu ina sanye da Riga da zani na atamfa da dankwali kaina na maida kasa ga Ahmad bayana na goya shi.
Anty mahma ta bude murya tana Fadin”Fa’iza ina kunshi ina gyaran kai..? Haka za’a dauko miki amaryan a ganki yarkace yarkace.?
Ban ce komai ba saboda basan me zan ce musu ba  halisa tace”Ko Saboda ba anan Amaryan zata zauna ba ne shiyasa kika zauna ba wani gyara..?
Anty Mamah tace”Wannan ba Hujja ba ne..ya kamata ko kunshi tayi saboda gyaran kanta da kanta Halisa”
Ni dai kaina na kasa ban ce komai ba kamar daga sama sai da ya Ishaq ya shigo Gidan yana waya kamar Sauri ma yake yi Anty Mahma ta tsaida shi ya katse wayar yana Fadin”Mahma jira na fa ake yi a waje”
Da Sauri ta mike tana fadin”Ya ishaq me zan gani haka Uwargida ba kun shi ba gyaran kai anya zakayi adalci kuwa..?
Kallona yayi sama da kasa ina ganinsa ta kasan idona sannan ya kwashe da Dariya kafin yace”Tab a bakin Fatar Fa’iza daman in akayi mata kunshi zai fito?
Ba ni kad’ai ba hatta su sai da mganar ta musu wani yam!
Ina gani suna kallon juna ita da Halisa suka kuma kalleni sai na nuna kamar ban ji me yace ba,menene sabo acikin mganarsa a wajena a wajen su ne sabo.
Anty Halisa ne tace”Kai Uncle akwai ma wadanda suka fi Fa’iza bakin fata kuma suna kunshi ko ita da kake ganin bakinta ka saki kudi a sama  mata mayuka masu kyau da Tsada kaga yadda Fatarta zata goge tayi Fresh kamar ba ita ba,ko Anty Mahma”?
Kai ta gyad’a kafin tace”Sosai ma yadda mayukan gyaran jiki da na fita suka cika Duniya ai da yawan mata ma ba Farin fatar su bane karawa suke da kwaskwarima”
Baki ya tabe kafin yace”Haka kurum na ba’ta kudina kan wannan abar.”
Ya fada ya nuna ni da baki kafin yace”ko an yi mata ba kyau zai yi ba asaran kudi na kawai zan yi sannan ku daina cewa wai farin wasu har da kwaskwarima na Zeey din’a  Inganttace ne babu algus,daga mahaifiyarta har mahaifinta Haifaffun Fulanin Adamawa ne”
Halisa tace”Uncle baka taba nuna mana Hoton ta ba”
Ina kallom su ya duba a waya ya nuna mata ta kallah ta kara kalla kafin tace”She is so Beautifull”
Baki ya washe yana jin Dadi Anty Mahma ya mikamawa ta karb’a tana Fadin”Hoto ba zahiri ba ne sai mun ganta ido da ido..”
Dariyan jin Dadi yayi kafin yace”Zaku ganta sati uku zamu yi zamu zo gaisheku in sha Allahu”
Sukace Allah yasa Daganan ya shiga Shashensa ya Dauko abu a leda ya Sake fita suma basu Dade ba sukamin Sallama suka tafi Anty mahma dai kallona kawai tayi tace min kiyi hakuri Fa’iza nayi mata mirmishi kawai ban ce komai ba.
Washegari sai ga Yaya Asiya ta Diro ita da Hafsah da Anty Nasara Goggo karofi ta rantse tace bazata zo ba Tunda dai Mama bata gayamata ba ayi sha’ani Lafiya.
Goggon karofi ta basu kayan miya da yawa sun zo min da shi,Sannan Yaya Asiya ta zo min da kayan kamshin girki da su kori saboda sana’ar da take yi a chan kano kenan Anty Nasara tazo min da less sabo dinkin Buba mai Tsada ta dinkamin kamar in yi kuka Allah Sarki dan’uwa mai rana.
Hafsah kuma ta tsifemin kai ina ta cewa bazan yi ba Anty Nasara tace”Zauna fa’iza ta tsefe miki ki wanke sai ayi miki kitso ki gyara jikin ki ba domin auran da mijinki zai yi ba Sai Domin kema kiji Dadin jikin ki”
Mganar ta yasa na zauna ta tsefemin kai Ahmad na Hannun Yaya Asiya su Amira kuma Daga makaranta basu Dawo gida ba da Jamal ya Dauko su da Motar Babansu gidan Mama ya sauke su tunda naji su shuru.
Ina ta tambayan su Ya mariya sukace zata taho dinki ne ba’a karisa ba ta tsaya karbowa
Da daddare kuma sai gata lokacin har Hafsah tamin kitso tana min yanka Salatif din da zata zana min dayake tana koya,Ko da Yaya mariya ta iso sun wanke kayan miya har sun bada nika sun tafasa sun tambayeni Cafanen girki nace bai bani komai ba kuma bai ce komai ba.
Yaya Asiya tace”Fa’iza kuma baki mai mgana ba..?
Anty Nasara tace”Ban da abun ki Asiya sai tayi mai mgana ai yasan ya kamata..?
Yaya mariya na gefe ta tabe baki bata dai yi mgana ba hira suka cigaba da yi bayan sun bar mganar acikin Hiran ne Yaya mariya tace ita ta fadama Tamadina Ya ishaq zai kara aure tace mata naje ammh ban fada mata ba Cikin Sanyina nace”Kawai sai na fada mata mijina zai kara aure..?
Duka sai suka kalleni Cikin Tausayawa ammh basu ce komai ba
Sai Dare Ya ishaq ya shigo gida Daman ina ta fargaba,ban san wani Rashin mutumci zai yi ba in yaga Yaya mariya agidan ba,Aiko da ita ya fara cin karo ta fito daga dakina,kallon kallon suka yi ma juna ni kuma ina falo zaune kafafuwana cikin leda Tunda an saka Lalllin,Hafsah ke gefena ta na sakamin na Hannu,jikina ya fara rawa bana so ya wulantamin yar’uwa,Hafsah ce ta gaishe shi ya amsa kamar bai santa ba Yaya mariya kuwa kamar bata gan shi ba haka tazo ta wucesa Ina ganinsa ya Dago yamin wani kallo ni kuma sai na sadda kaina kasa jikina na rawa fitowar su Yaya Asiya yasa bai yi mgana ba suka gaisa har zai shige shashen shi Anty Nasara tace”Ishaq wai me zamu dafa ne na taron Fa’iza gobe..??mun zo mun ga ba komai na cefane ko a wani waje za’a Dafa abincin namu ci ne kawai..?
Ta karishe fad’a cikin Zolaya kansa yasosa kafin yace”Na sha’afa ne ammh bari zan kira Mama ko Anty Binta”
Daga haka ya shige Ciki ya bar mu nan suka bisa da kallon mamaki,Ni dai gabana sai fad’i yake kada ya yi Tijaransa a gabansu,Kunshin da na saka ya Ceceni Domin sai chan Dare na cire sa kuma ya riga ya kwanta sai ban nemesa ba na yi sallar isha’i nayi shirin kwanciya ni da Yaya Asiya muka kwana Daki d’aya Yaya mariya da Anty Nasara da Hafsatu suka kwana Daki d’aya.
Kwana tayi bani baki da Shawarwari ina jinta kuma ina Dauka kalmar dai guda Dayace nayi hakuri to in ban yi hakuri ba ya zan yi..?
Da Safiyar ranar asabar karfe tara na Safe tawagan ango da waliyansa suka mika ko sallama Ya Ishaq bai min bai,bai kuma barmin komai ba,ina wanka naji su Anty Nasara na mganar sun fita shi da Jamal,a tunanin su zai dawo sai zuwan Badariya ta tabbatar da sun mika Hanya kuma ba dawowa zai yi ba Tunda chan amaryan zata zauna.
Ban yi amfani da kayan da Anty Binta ta bani ba Domin Yaya Asiya ma ta dinkama na atamfa mu hudu har da Hafsah dinkin ne Yaya mariya ta tsaya  ta karbo mana.
Ganin har sha Daya tayi kawai sai nace su Dafa sauran shinkafar data ragemana Daman bata wuce tiya hudu ba Tunda Ya ishaq din bai ce komai ba kayan miya kuma sai suyi miya dashi Yaya mariya sai fada take tana fadin”Haba aiko Dai darajan kashin miya ma samu”
To kafin ma a tashi a d’aura sai ga Anty Binta tazo da mganar chan gidan Mama zamu koma ayi bikin gabadaya.
Yaya mariya ta Daka tsalle tace wlh ba wanda ya isa shikenan saboda sun maidani banza a banza taron ma ni da Dangina sai an yi min iko da shi.
Anty binta ko taki tafiya tace kafarta kafarmu ai nan din da gidan Maman duk D’aya ne
Su Yaya Asiya suka shiga tsakaninsu ammh sun fara cacan baki,nayi kuka kukan bakinciki da wannan tozarcin da aka shiryamin Yaya mariya tayi rantsuwan bazata je gidan Mama ba,ko sallama haka ta Dauki kayanta ta wuce karofi ni da Yaya Asiya sai Anty Nasara da Hafsatu dake goye da Ahmad muka tarkata zuwa gidan mama a ka kulle gidan key din ma na Hannun Anty Binta.
Dakin Badariya muka sauka Saboda nan muke da Daraja,kallon mutumci cikin Dangin Mama ko kawayenta ba wanda yayi mana gida cike da mutane sai harkan arziki akeyi su Amir sun shige cikin yara sa’o’in su suna ta wasa Anum ta saka anko Mutsy kuma kayan yan kanti Amir dai ban gansa ba Anum tace dashi Uncle Jamal suka tafi.
Abinci ma sai chan da Rana aka kawo mana shima sai da Anty Mahma ta shigo ne taganmu baki bude tace an kawo mana abinci mukace a’a ita ta fita ta samo mana waina da Jallop din shimkafa sai alala.
Duk yadda naso na Daure ma wannan wulakancin na kasa har ta su Yaya Asiya abun ya tabasu suna tare dani sun kasa fita Hafsatu ce Badariya ta jata.
Kawayen Mama sai dai su lekomu suna Dariya a wulakance,sanda yan Daurin aure suka kira sukace an Daura aure haka Anty Binta ta rika rangad’a gud’a ita da kawayenta itama Mama ance har da rawa sai da ta taka Anty Nasara ta kalleni ina ta sharan kwallah ta dafani kafin tace”Ki yi hakiru Fa’iza ki bar kuka..Watarana sai Labari”
Yaya Asiya abun ya ciwota sai ta kasa ma mgana har da kidan kwarya sai da yan yamai sukayi sannan da Daddare suka kure kid’a da wakar Bikin Ishaq da zainab suna rawa ni dai ina kan sallaya tun bayan da nayi sallar isha”i ban Daga ba ina kai ma Allah kukana.
Washegari ma Anty Mahma ne ta kawo mana kosai da koko muna gama karyawa su Yaya asiya suka yi Haraman Tafiya na kallesu a marairaice kafin nace”Tafiya kuma zaku yi..?
Yaya asiya tace”Kiyi hakuri Fa’iza ya zama Dole ga Hafsah nan ta zauna sai gobe sai ta dawo mukan yau zamu tafi in sha Allahu”
Ban hanasu ba domin suna da gaskiya gwara kayi nesa da in da ba’asan Darajan ka ba.
Da zasu tafi har Dakin Mama sukaje sukayi mata fatan alheri Hajiyar Dala bata ta nan da ita aka tafi Abuja ita zata tarbi Amarya ance suna hanya yau zasu dawo.
Mama sai mgana take har tana fadin”Nasara goggon taku dai taki zuwa to ku shaida mata an daura auran ba’a fasa ba”
Su dai basu mayar mata da mgana ba suka musu sallama suka kama Hanya ransu ba Dadi.
Naso aranar na koma gida Anty Binta tace ban isa ba,Sai an watse taro Sai Yammah mutanen abuja suka Dawo Hajiyar Dala murya har waje ta na bada Labarin gidan arzikin da Ya Ishaq ya nemi aure tazo da Turamen tamfa na iyaye guda goma da kayan gara mota guda har da shaddodi da kuloli kayan uwar miji da Uban miji Robobi cike da kayan fulawa har da nakiya da alkaki.
Nima Anty Binta ta kawomin alkaki da Cin cin,Sai kula mai biyu guda daya na karb’a na saka albarka a bakin Badariya nake jin har da Turmin Atamfa akace abani Mama ta Dauke tace ba za’a abani ba araina nace ko an bani bazan Daura ba ai ban dace da kayan alfarma irin shi ba da su yafi Dacewa.
Agidan muka kara kwanaa sai Ranar Lahadi da yammah muka koma gida bayan ni da Hafsah mun zage mun gyara gidan Mama tas sannan Anty Binta ta bani key din gidan na Tattara duka ya’yana  muka koma gidana Hafsha kuma nace ta bari sai washegari sai ta tafi.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here