Kana Ganin Cire Tallafin Man Fetur Da Zai Sa Farashi Ya Tashi Da Tinubu Zai Yi In Ya Ci Zabe Abu Ne Mai Kyau?

Kana Ganin Cire Tallafin Man Fetur Da Zai Sa Farashi Ya Tashi Da Tinubu Zai Yi In Ya Ci Zabe Abu Ne Mai Kyau?

 

Ina Cin Zabe A 2023 Zan Cire Tallafin Man Fetur, Farashi Zai Tashi---Tinubu 

 
Dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar, All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya yi alkawarin cire tallafin mai yana hawa mulki. 
A takardar manufofinsa da ta yadu ranar Juma'a, Tinubu yace a cikin wata shida na farko zai aiwatar da sabuwar dokar PIA, zai cire tallafi kuma zai samar da wasu sabbin ka'idoji don janyo hankalin masu zuba jari. 
"Zamu cire tallafin man fetur amma zamu samar da hanyoyin taimakawa mutane."
"Zamuyi hakan ta zuba kudin tallafin wajen gine-gine, aikin noma, shirye-shiryen jin dadi wanda ya hada da gina titi, rijiyar burtsatsai, rage kudin mota, ilimi da kuma kiwon lafiya." 
"Bayan cire tallafin mai, zamu mayar da hankali wajen gyara matatun man kasa tare da hada kai da wasu kasashe masu arzikin man fetur a fadin duniya."