Kan Zargin Dukan mahaifnsa ya gurfana gaban kotu shi da mahaifiyarsa

Kan Zargin Dukan mahaifnsa ya gurfana gaban kotu shi da mahaifiyarsa
Uwa da danta, wadanda ake zargin sun lakaɗa wa da mahaifin yaron duka sun gurfana a gaban wata kotun Majistare da ke Ojo a jihar Legas.
Wadanda ake tuhumar – Chukwudi Igbonekwu, mai shekaru 19; da Ngozi Igbonekwu mai shekaru 49; an gurfanar da su a gaban wani alkali L.K.J Layeni, kan tuhume-tuhume biyar da su ka hada da hadin baki, da cin zarafi, barazana ga rayuwa, da haifar da rashin zaman lafiya.
Sai dai kuma dukka sun musanta laifin da ake tuhumarsu da shi.
Dan sanda mai shigar da kara, ASP Simon Uche, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a ranar 18 ga watan Janairu a unguwar Iyana Itire da ke Ajangbadi a Ojo.
Ya yi zargin cewa bayan wata taƙaddama da aka samu, mahaifiyar da danta sun hada baki don cin zarafin mai karar, mai suna Edwin Igbonekwu.
Ana zargin wadanda ake tuhumar da karya kofar gidan, tare da yi wa mai mutumin duka tare da yi masa barazanar kisa.
Kotun dai ta bayar da belin wadanda ake kara a kan kudi Naira 200,000 kowanne, tare da tsayayyu biyu kowannen su.
Alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 19 ga watan Fabrairu.