Kamfanonin jiragen sama sun dakatar da zirga-zirga zuwa Isra'ila

Kamfanonin jiragen sama sun dakatar da zirga-zirga zuwa Isra'ila

Yayin da Isra'ila ta sake buɗe sararin samaniyarta a ranar Lahadi, wasu kamfanonin jiragen sama na Turai sun dakatar da zirga-zirgar jiragensu zuwa Tel Aviv bayan komawa zirga-zirga a yankin makonni kalilan da suka gabata.

EasyJet ya dakatar da zirga-zirgar jiragens zuwa Tel Aviv a ranakun Lahadi da Litinin.

Shi ma kamfanin jirgin sama na Wizz Air ya dakatar da zirga-zirgar jiragensa tsakanin Birtaniya da Isra'ila a ranakun Lahadi da Litinin, "bayan rikici da ake fuskanta a yankin".

Wani mai magana da yawun kamfanin jirgin ya ce za a mayar wa dukkan fasinjojin da abin ya shafa kuɗaɗenu ko ba su zaɓin sake yin wani tikiti .

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, kamfanin jiragen sama na United Airlines - wanda shi ne babban kamfanin jiragen sama na Amurka da ya koma zuwa Isra'ila tun bayan ɓarkewar rikici - shi ma ya soke tashin jirgin da zai yi a yau Lahadi tsakanin Newark da Tel Aviv