Kamfanin Hasken Wutar Lantarki Kaduna Electric Ya Baiwa Al'ummar Sakkwato Da Kebbi Haƙuri

Kamfanin Hasken Wutar Lantarki Kaduna Electric Ya Baiwa Al'ummar Sakkwato Da Kebbi Haƙuri
Daga Abbakar Aleeyu Anache.
Kaduna Electric ya baiwa abokan huldarsu hakuri na dauke wutar lantarki acikin Sakkwato da kebbi.
Electric ya bayyana hakan ne a shafinsa na sada zumunta Facebook cewa suna baiwa abokan huldarmu hakuri dake jihohin Sakkwato da kebbi na rashin wuta da ake fuskanta a halin yanzu.
Wannan ya kasance ne sakamakon lahani na kayan aikin wutar lantarki da aka samu a lokacin iska mai nauyi acikin kebbi da Sakkwato jiya in ji sanarwar.
Kungiyoyin injiniyoyin mu a cikin jihohinmu biyu suna aiki tukuru domin ganin an gyara matsalar na kayyakin da suka lalace dan dawowa da hasken lantarki ba tare da bata lokaci na wuraren da abin ya shafa
Muna kara ba abokan huldarmu hakuri akan duk wani tsaiko da rashin wutar zai haifar da kuma bada tabbacin dawowa da hasken lantarki da zaran an kammala aikin gyare-gyaran.