Kakakin majalisar Sakkwato ya ƙauracewa zaɓen shugabanin APC

Ya ce "Mun amince Sakkwato za mu yi zabe babu hamayya waton na amincewa,  amma ba  mu hana wanda yake son ya shiga zabe ya fito ba sai a gudanar da zabe wanda ya samu nasara shi ne na jama'a." a cewarsa.  Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen  a jihar Sakkwao Abubakar Suleman Iyan Akko a jawabinsa ga jagororin jam'iya ya ce  sun zo ne amadadin hidikwatar APC  don  gudanar da zaben shugabanni kuma sun gamsu da tsarin da suka tarar.

Kakakin majalisar Sakkwato ya ƙauracewa zaɓen shugabanin APC
Aminu Muhammad Achida

 
Kakakin majalisar jihar Sakkwato Alhaji Aminu Muhammad Achida ya ƙauracewa zaɓen shugabannin APC da aka gudanar a jihar.
A binciken da Managarciya ta gabatar  ta tabbatar   shugaban majalisar bai halarci wurin zaɓen da aka gudanar a hidikwatar jam'iya ba.

Aminu Muhammad bai halarci taron masu ruwa da tsaki na jam'iyar kafin soma zaɓen duk da shugaban riƙo na jam'iyar a Sakkwato Isah Sadiƙ Achida ya ce sun gayyaci Kakakin majalisar ba su san dalilinsa na kin halarta ba. 
 

Isah Sadik Achida ya yi wa kwamitin zaben  barka da zuwa amadadin masu ruwa da tsaki na jam'iyar.

Ya ce "Mun amince Sakkwato za mu yi zabe babu hamayya waton na amincewa,  amma ba  mu hana wanda yake son ya shiga zabe ya fito ba sai a gudanar da zabe wanda ya samu nasara shi ne na jama'a." a cewarsa. 

Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen  a jihar Sakkwao Abubakar Suleman Iyan Akko a jawabinsa ga jagororin jam'iya ya ce  sun zo ne amadadin hidikwatar APC  don  gudanar da zaben shugabanni kuma sun gamsu da tsarin da suka tarar.

Managarciya ta yi kokarin jin tabakin shugaban majalisar dokoki Aminu Achida sai dai abin ya ci tura kuma wayar shi a kashe.