Kada Ku Kuskura Ku Zabi Shugabannin da Ba Su Cancanta Ba---Sarki Sanusi

Kada Ku Kuskura Ku Zabi Shugabannin da Ba Su Cancanta Ba---Sarki Sanusi


Sarkin Kano na 14, kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya ba 'yan Najeriya shawarin irin shugabannin da ya kamata su zaba a zaben 2023 mai zuwa. 

Muhammadu Sanusi II, ya ce ya kamata 'yan Najeriya natsu su zabi shugabannin da ke da kwarewa ta gudanar da kasa a zabe mai zuwa, kuma su kauda batun kabilanci, TheCable ta ruwaito.
Sanusi ya bayyana hakan ne a jiya Laraba 24 ga watan Agusta a jihar Legas taron The August Event 2022 da gidauniyar Moses Adekoyejo Majekodunmi tare da hadin gwiwar Asibitocin Santa Nicholas suka shirya. 
“Ya kamata a titsiye 'yan siyasa domin su fadi shirinsu kan asibitoci da ilimi da sauran muhimman bangarorin da suke da koma baya a kasar nan. 
“Gwamnati dai ta daina mutunta wannan sana’ar kuma babu adadin kudaden da za a kashe a fannin ilimi ta albashi a kasar nan da zai kawo sauyi. 
Likitoci da malamai ya kamata gansu cikin rayuwa mai kyau da mutuntawa.
" Ya kuma bayyana cewa, bangare mafi kyau da zai gyara kowace kasa a duniya shi ne ilimi, inda ya koka da cewa, akwai bukatar martaba ilimi da kiwon lafiya a Najeriya.