Ka san dalilin shanyewar ƙafa bayan allura a ɗuwawu?

Ka san dalilin shanyewar ƙafa bayan allura a ɗuwawu?

Shanyewar ƙafa matsala ce da ke faruwa sakamakon lahani ga jijiyar laka da ake kira da 'sciatic nerve' wace ke kai saƙonni zuwa wasu tsokokin ƙafa.

Wannan jijiyar laka ta fito daga laka ne sai ta biyo ta cikin ƙashin ƙugu sannan ta ratso ta cikin tsokokin ɗuwawu zuwa ƙafa har tafin sawu.

Wannan matsala na faruwa ne idan aka kuskure aka tsira allura a kan jijiyar lakar yayin allura a ɗuwawu, ko idan ruwan allurar ya tunzira jijiyar lakar, ko kuma idan allurar ko ruwan allurar ya kawo kumburi a kewayen jijiyar lakar wanda hakan na iya danne ko shaƙe ta har aikinta ya samu cikas.

Waɗanda suke da haɗarin samun wannan matsala sun haɗa da:

1) Wanda bai bayar da haɗin kai ba yayin yin allurar, musamman ƙananan yara da ma manyan masu tsoron allura.

2) Mai rama sosai.

3) Faɗawa hannun wanda bai ƙware ba.

4) Da kuma wanda tsautsayi ya faɗa wa.

JAN HANKALI: Daga cikin matsalolin da ke ƙara afkuwar shanyewar ƙafa bayan allura, musamman ga yara, akwai al'adar nan ta tsorata yara da yi musu allura idan suna ƙiriniya ko kuma idan ana so su yi ko bar wani abu. Tsorata su da allura yana shiga tunaninsu cewa allura aba ce mai ciwo sosai. Saboda haka, duk lokacin da za a yi musu allura suke tsorata har su fara zille-zille. Wannan zille-zille ne kuma ke sa allura ta sauya hanyarta daga tsoka zuwa jijiyar laka.

Alamomin wannan matsala na faruwa ne a dukan rassan jijiyar lakar a ƙafa nan take ko bayan wani ɗan lokaci.

Alamomin sun haɗa da:

1. Matsanancin ciwo

2. Sagewa

3. Shanyewar tafin sawu

3) Rauni ko rashin ƙwarin ƙafa

4) Rashin ji a fata idan aka taɓa

5) Wahalar tafiya: ɗingishi, jan ƙafa da sauransu.

Da zarar an lura da waɗannan matsaloli da aka ambata a sama, a gaggauta sanar da jami'in lafiyar da ya yi allurar domin ɗaukar matakan gaggawa. Wannan matsala ana warkewa sumul kamar ba a yi ba. Sai dai jinkirin zuwa asibiti na iya nakasa ƙafar.

Game da shanyewar ƙafa likitocin fisiyo (Physiotherapists) ne ke amfani da hanyoyin ƙwarewa domin yi wa jijiyar lakar da tsokokin ƙafar ƙaimi har aikinsu ya dawo yadda ya kamata.