Hakan na zuwa ne bayan tsauraran matakan da ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS ), ke ci gaba da ɗauka kan sojojin.
Kamfanin dillancin labaran AP ya yi rahoto cewa, wani babban jami’in diflomasiyyar Amurka ya bayyana cewa, sojojin na Nijar sun yi barazanar kashe Bazoum idan ECOWAS ta tura sojoji kasar da zummar dawo da mulkin dimokuradiyya.
Biyo bayan juyin mulkin da sojojin na Nijar suka yi, ƙasashen ECOWAS da ke maƙwabtaka da jamhuriyar Nijar, sun yi Allah wadai da lamarin tare da bai wa sojojin kwanaki bakwai su maida mulki.
Sai dai sojojin da suka yi juyin mulkin sun yi biris da umarnin na ECOWAS, wanda hakan ya janyo wani taro na musamman da ƙungiyar ta yi a ranar Alhamis da ta gabata.
Akwai wasu matakai guda huɗu masu tsauri da ƙungiyar ta ECOWAS ta ɗauka tun bayan juyin mulkin, waɗanda ake ganin sun fusata sojojin na Nijar. Matakan su ne:
1. Aika saƙon gargaɗi ga ƙasashen da ke goyon bayan sojojin Nijar Kungiyar ECOWAS ta aikawa ƙasashen da ke goyon bayan sojojin juyin mulkin na jamhuriyar Nijar gargaɗi mai zafi dangane da abinda suka yi. Ƙasashen da ECOWAS ta aikawa saƙon gargaɗin sun haɗa da Mali, Burkina Faso, Guinea, Mali da Guinea Bissau.
2. Neman haɗin kan AU da UN Mataki na gaba mai tsauri da ake ganin ya fusata sojojin Nijar shi ne, neman goyon bayan Tarayyar Afrika (AU), da Majalisar ɗinkin Duniya (UN).
Idan AU da UN suka goyi bayan ECOWAS, ta hanyar marawa matakan da ta ɗauka baya, hakan zai iya janyowa sojojin na Nijar matsin lamba daga 'yan ƙasa, saboda da ƙuncin rayuwar da za su shiga.
3. Tabbatar da matakan da aka ɗauka a baya A zama na biyu na musamman da shugabannin ECOWAS suka yi, sun yanke shawarar tabbatar da matakan da suka ɗauka kan Nijar da ƙwawayenta a baya. Daga cikin matakan akwai rufe iyakoki, sanya takunkumin tafiye-tafiye da kuma riƙe kadarorin mutanen da ake tunanin suna taimakawa masu juyin mulkin.